Da Ɗumi-Ɗumi: Ba Za’a Ga Watan Sallah Ba Sai Ranar Laraba, Inji Hukumar NASRDA

Da Ɗumi-Ɗumi: Ba Za’a Ga Watan Sallah Ba Sai Ranar Laraba, Inji Hukumar NASRDA

- Hukumar binciken sararin sama ta ƙasa NASRDA tayi hasashen cewa jinjirin watan shawwal ba zai bayyana ba sai ranar Laraba 12 ga watan Mayu

- Hukumar tace idan har hasashen ta ya zama gaskiya, musulmai zasu gudanar da sallar Eid Fitr a ranar Alhamis 13 ga watan Mayu

- Wannan na ƙunshe ne a wani jawabi da kakakin hukumar NASRDA, Dr. Felix Ale ya fitar, inda ya bayyana cewa watan zai fara fitowa fili ne da ƙarfe 8:30 na safiyar Laraba

Hukumar binciken sararin samaniya ta ƙasa (NASRDA), tace bayyanar jinjirin wata na gaba, wanda zai nuna ƙarshen watan azumin ramadana, zai fito ne ranar Laraba 12 ga watan Mayu 2021, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Gwamnan Ondo Zai Buɗe Sabon Masallaci Na Farko da Aka Gina a Cikin Gidan Gwamnatin Jiharsa

Idan hakan ta faru kamar yadda hasashen NASRDA ya bayyana, to za'ai hawan idin ƙaramar sallah (Eidil Fitr) ranar Alhamis 13 ga watan Mayu.

A wani jawabi da kakakin hukumar NASRDA, Dr. Felix Ale, ya fitar yace daga binciken da suka gudanar za'a gama haɗa watan da misalin ƙarfe 8:00 na daren ranar Talata.

Da Ɗumi-Ɗumi: Ba za'a ga watan Sallah ba sai ranar Laraba, Inji Hukumar NASRDA
Da Ɗumi-Ɗumi: Ba za'a ga watan Sallah ba sai ranar Laraba, Inji Hukumar NASRDA Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Yayin da jinjirin watan zai bayyana a sararin samaniya a Najeriya da misalin ƙarfe 8:30 na safiyar ranar Laraba 12 ga watan Mayu.

Ale ya ƙara da cewa, jinjirin watan bazai ganu da safiyar Laraba da idanu ba saboda ƙanƙantarsa da kuma hasken wannan lokacin.

Amma zai fito yadda za'a iya ganinsa da yammacin ranar ta Laraba daga karfe 6:21 zuwa ƙarfe 7:42 na dare bayan faɗuwar Rana.

A jawabin da ya fitar, Ale yace:

"Bayyanar jinjirin watan a jihohin ƙasar nan zai kasance kamar haka: Za'a fara ganin watan a garin Yola dake Adamawa daga 6:51-6:57 na yamma, sai kuma Maiduguri a jihar Borno daga 6:53-6:59 na dare."

"Hakanan kuma watan zai bayyana a Jalingo dake jihar Taraba daga 6:26-7:02 na dare, sai kuma jihar Yobe da Gombe daga 6:28- 7:04 na dare da 6:29- 7:05 na dare a jere. A Abuja babban birnin ƙasar nan, jinjirin watan zai bayyana ne daga 6:45-7:27 na dare."

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Yan Sanda Sun Kuɓutar Da Mutum 30 Cikin 40 Da Aka Sace Wurin Tahajjud a Katsina

"Watan zai bayyana a jihar Kano da Sokoto daga ƙarfe 6:42- 7:19 na dare; da 6:57- 7:43 na dare a jere. Hakanan kuma a Abekuta dake jihar Ogun, watan zai bayyana a sararin sama ne daga 6:56- 7:33 na dare."

Ya ƙara da cewa:

"A jihar Katsina jinjirin watan zai bayyana daga 6:47-7:24 na dare, yayin da a Plateau da Kaduna watan zai fito daga 6:38- 7:14 na dare, da 6:44- 7:21 na dare a jere. Hakanan watan zai fito a fili a jihar Enugu daga 6:38-7:15 na dare, sai kuma Birnin Kebbi daga 7:00-7:37 na dare."

"Sauran jihohin kuwa ana hasashen jinjirin watan zai bayyana ne yadda ido zai iya ganinsa daga 6:21-7:42 na dare, dukkan su a ranar Laraba 12 ga watan Mayu, 2021 kamar yadda bincike ya nuna."

A wani labarin Kuma Wasu Yan Bindiga Sun Ƙone Ofishin Jami’an Tsaro da Motarsu, Sun Hallaka Mutum Biyar

Aƙalla mutum biyar ne Suka rasa rayukansu a wani sabon hari da yan bindiga suka kai Ƙauyen Izubulu dake cikin jihar Anambra.

Rahotanni sun bayyana cewa yan bindigan sun ƙona ofishin jami'an tsaron sa kai da motar hawan su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel