Da Ɗumi-Ɗumi: Wasu Yan Bindiga Sun Ƙona Ofishin Hukumar NDLEA a Jihar Abia
- Wasu yan bindiga da ba'a san ko su waye ba sun kai wani mummunan hari ofishin hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi NDLEA a jihar Abia
- Yan bindigan sun ƙona ofishin NDLEA ɗin dake Amekpu ƙaramar hukumar Ohafia
- Kwamandan NDLEA na jihar Abia, Mr Akingbade Bamidele, ya tabbatar da kai harin amma yace babu wanda wutar ta ritsa dashi
Wasu yan bindiga da ba'a san ko su waye ba sun kai hari ofishin hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi NDLEA dake Amaekpu ƙaramar hukumar Ohafia jihar Abia da safiyar yau Talata.
KARANTA ANAN: Kungiyar Inyamurai Ta Ɗau Zafi Bisa Zargin Jami’an Soji Na Shirya Mata Wata Maƙarkashiya
A yayin harin, yan bindigan sun cinnawa ofishin wuta, kamar yadda jaridar Dailytrust ta ruwaito.
Kwamandan hukumar NDLEA na jihar, Mr Akingbade Bamidele, shine ya tabbatar da faruwar lamarin amma yace babu wanda lamarin ya ritsa dashi.
Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan yan bindiga sun kai makamancin irin wannan harin ga ofishin hukumar zaɓe da kuma na yan sanda a jihar tare da ƙona ofisoshin.
KARANTA ANAN: Wike Ya Bada Kyautar Miliyan N220m Ga iyalan Jami'an Yan Sanda 11 da Aka Kashe
Ana cigaba da samun ƙarin hare-hare akan jami'an tsaro da kuma wasu kayayyakin gwamnati a yankin kudu maso gabas da kuma kudu maso kudancin ƙasar nan tare da kashe wasu jami'an yan sanda da lalata ofisoshin hukumar ta yan sanda.
Sai-dai ana zargin ƙungiyar masu fafutukar kafa ƙasar biyafara IPOB da ɗaukar nauyin kai waɗannan hare-haren.
A wani labarin kuma Jami’ai 21 Aka Kashe a Harin da Yan Bindiga Suka Kai Akwa Ibom, Inji Kwamishina
Hukumar yan sanda a jihar Akwa Ibom ta bayyana wa gwamnan jihar cewa jami'an yan sanda 21 ne suka rasa rayukansu a harin da yan bindiga suka kai musu a jihar.
Kwamishinan yan sandan jihar, Amiengheme Andrew, shine ya bayyana wa gwamnan a wata ziyara da ya kai hedkwatar su domin yin ta'aziyya. Gwamnan ya sanar da bayar da kyautar kuɗi 60 miliyan ga iyalan gwarazan yan sandan.
Asali: Legit.ng