Jami’ai 21 Aka Kashe a Harin da Yan Bindiga Suka Kai Akwa Ibom, Inji Kwamishina

Jami’ai 21 Aka Kashe a Harin da Yan Bindiga Suka Kai Akwa Ibom, Inji Kwamishina

- Hukumar yan sanda a jihar Akwa Ibom ta bayyana wa gwamnan jihar cewa jami'an yan sanda 21 ne suka rasa rayukansu a harin da yan bindiga suka kai musu a jihar

- Kwamishinan yan sandan jihar, Amiengheme Andrew, shine ya bayyana wa gwamnan a wata ziyara da ya kai hedkwatar su domin yin ta'aziyya.

- Gwamnan ya sanar da bayar da kyautar kuɗi 60 miliyan ga iyalan gwarazan yan sandan da suka rigamu gidan gaskiya a wajen ƙoƙarin tsare jihar

Hukumar yan sanda a jihar Akwa Ibom ta bayyana cewa jami'an yan sanda 21 ne yan bindiga suka hallaka a hari daban-daban da suka kai faɗin jihar.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Ba Za’a Ga Watan Sallah Ba Sai Ranar Laraba, Inji Hukumar NASRDA

Kwamishinan yan sandan jihar, Amiengheme Andrew, shine ya bayyana haka a ranar Litinin yayin da yake jawabi ga gwamnan jihar, Udom Emmanuel, a hedkwatar yan sanda, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Gwamna Udom Emmanuel, ya kai ziyara hedkwatar yan sandan ne domin yayi ta'aziyya ga iyalan gwarazan yan sandan da suka rasa rayukansu.

Jami’ai 21 Aka Kashe a Harin da Yan Bindiga Suka Kai Akwa Ibom, Inji Kwamishina
Jami’ai 21 Aka Kashe a Harin da Yan Bindiga Suka Kai Akwa Ibom, Inji Kwamishina Hoto: thewillnigeria.com
Asali: UGC

Kwamishinan yan sandan ya faɗawa gwamnan cewa hukumar ta rasa motocin hawan ta 11 da bindigogi 7 a hare-haren.

KARANTA ANAN: Gwamnan Ondo Zai Buɗe Sabon Masallaci Na Farko da Aka Gina a Cikin Gidan Gwamnatin Jiharsa

Kwamishinan yace: "Jami'an mu 21 ne suka riga mu gidan gaskiya sanadiyyar harin da yan bindiga suka kai musu a lokaci daban-daban."

"Hakanan kuma motocin mu 11 sun salwanta a yayin hare-haren, sannan mun rasa bindigogi 7."

"Nayi matuƙar farin ciki da wannan ziyara, kuma munyi alƙawarin cewa hukumar mu zata cigaba da yin iyakar bakin ƙoƙarinta wajen kare jihar daga dukkan matsalolin tsaron da take fama dasu."

A yayin wannan ziyarar, gwamnan ya sanar da bada tallafin kuɗi 60 miliyan ga iyalan yan sandan da suka rasa rayuwarsu.

A wani labarin kuma NDLEA Ta Bankado Masu Safarar Miyagun Kwayoyi Ta Yanar Gizo, Ta Kama 5 a Abuja

Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta bankaɗo wasu gurɓatattun mutane dake safarar ƙwayoyi a yanar gizo.

A binciken da NDLEA tayi ta samu nasarar cafke mutane biyar a babban birnin tarayya Abuja ta hanyar ɗana musu tarko da siyan kayan su a yanar gizo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel