Yunkurin Fashi a Fadar Shugaban Kasa Ya Nuna Buhari Ba Zai Iya Tsare Najeriya ba, PDP

Yunkurin Fashi a Fadar Shugaban Kasa Ya Nuna Buhari Ba Zai Iya Tsare Najeriya ba, PDP

- Jam'iyyar PDP ta bayyana cewa, ta damu da kai hari da aka yi kusa da fadar shugaban kasa

- Ta ce, wannan na nuni karara cewa, shugaba Buhari bazai iya kare Najeriya daga barna ba

- Hakazalika jam'iyyar ta shawarci shugaban da ya yi kwaskwarima a tsarin tsaron Najeriya

Jam'iyyar adawa ta PDP ta bayyana firgici game da fashin da aka yi a kusa da fadar shugaban kasa, Aso Villa a babban birnin tarayya Abuja.

PDP ta nuna damuwa kan lamarin, tana mai zargin rashin iyawar shugaba Muhammadu ta fuskar bai wa kasar cikakken tsaro don kare rayukan al'umma.

A daren jiya Litinin ne fadar shugaban kasa ta fitar wata sanarwa ta hannun mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu cewa 'yan fashi sun afka gidan shugaban ma'aikata na shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari; lamarin da ya jawo cece-kuce.

KU KARANTA: 'Yan Kasuwa Sun Tafka Asara Bayan Mummunar Gobara da Ta Yi Kaca-kaca da Kasuwa

Yunkurin Fashi a Fadar Shugaban Kasa Ya nuna Buhari Ba Zai Iya Tsare Najeriya ba, PDP
Yunkurin Fashi a Fadar Shugaban Kasa Ya nuna Buhari Ba Zai Iya Tsare Najeriya ba, PDP Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

A wata sanarwa da Legit.ng Hausa ta ga PDP ta wallafa ta shafinta na Tuwita , ta ce: "PDP ta firgita da afkawar da 'yan fashi da makami suka yi a fadar shugaban kasa ta Aso Villa, tana mai cewa hakan yana kara nuna rugujewar tsarin tsaro a karkashin kulawar Shugaba Buhari."

Ta kuma bayyana matukar mamakin fashin duk da irin tsaro da ake bai wa fadar shugabanni a duk duniya.

"A duk fadin duniya, Fadar Shugaban kasa, a matsayin matattarar iko da mulkin kasa take, kakkarfa ce ta yadda da yakamata ace ta sami tsaro mara karfi.

"Saboda haka, duk wata matsalar rashin tsaro, musamman ta hanyar doka da oda, tana nuna wata alama ce mai hatsari ga tsaron kasar gaba daya."

PDP ta kuma nuna damuwarta: "Jam’iyyarmu ta damu cewa idan har Shugaba Buhari ba zai iya tabbatar da tsaron fadar Shugaban kasa ba, to kuwa ba bu tabbacin ikonsa na bai wa kasar kariya."

Karshe PDP ta yi kira ga shugaba Buhari da ya yi duba da tsarin tsaron kasar tare da tabbatar da daukar matakan da suka dace don inganta tsaro a fadin kasar.

KU KARANTA: Saboda Ayaba, Wani Soja Ya Bindige Dan Kasuwa a Jihar Zamfara

A wani labarin, Lai Mohammed, Ministan yada labarai da al'adu, ya ce 'yan bindigar da ke addabar kasar za su dandana kudarsu, TheCable ta ruwaito.

An samu matsalar yawaitar barnar 'yan bindiga a duk fadin kasar wadanda suka kai ga satar mutane tare da neman kudin fansa da kuma aikata fashi da makami.

Da yake jawabi a taron manema labarai a Legas a ranar Talata, Mohammed yace jami'an tsaron kasar sun fuskanci hare-hare na "rashin tunani" daga 'yan bindiga don cusa tsoro da haifar da rashin tsaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel