Fusatacciyar Mata Ta Sanya Maciji A Cikin Akwatin Gawar Mijinta Don Yin Maganin Wadanda Suka Kashe Shi

Fusatacciyar Mata Ta Sanya Maciji A Cikin Akwatin Gawar Mijinta Don Yin Maganin Wadanda Suka Kashe Shi

- An gano wata mutuniyar Ashanti tana saka maciji mai rai a cikin akwatin gawar mijinta a yayin jana’izarsa

- An bayyana a wurin jana'izar cewa dalilin hakan shi ne macijin ne ya kashe shi kuma dole ne a binne shi tare da shi

- Sai dai kuma, mutanen da suka san al'adun Akan suna bayanin cewa ana nufin yin maganin duk wanda ke da hannu a mutuwar mutumin

An ga wata mata 'yar kabilar Ashanti wacce ta fusata game da mutuwar mijinta tana sanya maciji a cikin akwatin gawarsa domin ya yi maganin duk wanda ke da hannu a mutuwarsa.

A cikin faifan bidiyan da ake yadawa a shafukan sada zumunta, an ga matar zagaye da wasu daga cikin danginta da masu alhini wadanda suka zo don ta’aziyyar mamacin.

KU KARANTA KUMA: Karya Ne El-Rufai Bai Taba Cewa Buhari Bai Cancanci Shugabancin Najeriya Ba – Gwamnatin Kaduna

Fusatacciyar Mata Ta Sanya Maciji A Cikin Akwatin Gawar Mijinta Don Yin Maganin Wadanda Suka Kashe Shi
Fusatacciyar Mata Ta Sanya Maciji A Cikin Akwatin Gawar Mijinta Don Yin Maganin Wadanda Suka Kashe Shi Hoto: @adomtv
Asali: Twitter

Sautin bayan fage ya ce macijin ya harbi harshen marigayin har sai da ya mutu, wannan ne ya sa matar ta ga ya dace ta binne shi tare da abin da ya kashe shi.

Kalli bidiyon a kasa:

Sai dai, da yawa waɗanda suka san al'adar sun bayyana cewa wannan don yin maganin duk wanda ke da alaƙa da mutuwar mamacin ne.

Misali, funghana_ ya ce:

"An yi amannar cewa mutumin bai yi mutuwar Allah ba, don haka ruhun macijin zai sari duk wanda yake da hannu a cikin mutuwarsa da zaran macijin ya mutu."

KU KARANTA KUMA: Ortom Ya Yiwa El-Rufai Wankin Babban Bargo, Ya Ce Yana Daya Daga Cikin Makiyan Najeriya Na Hakika

Bayan ta yi wasu yan surkulle, sai matar ta dauki macijin da ke rataye a wuyanta ta saukar da shi cikin akwatin yayin da take nuna alamun da ke nufin "ka yi maganinsu ba tare da tausayi ba".

A wani labarin, iftila'in ya faru ne a karshen mako a jihar Neja, biyo bayan hatsarin jirgin ruwan da ya faru a garin Tijana na karamar hukumar Munya da ke jihar wanda ya kai ga mutuwar mazauna kauye sama da 15 a cikin jirgin ruwan a cikin wani kogi da ke yankin.

Jirgin ruwan ya kife ne da misalin karfe 6:00 na yamma a ranar Asabar lokacin da ake zargin mazauna kauyen sun dawo daga wata kasuwar yankin da ke Zumba a karamar hukumar Shiroro ta jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel