Gwamna El-Rufai Ya Bayyana Abinda Ya Kamata Yankin Kudu Maso Gabas Ya Yi Don Lashe Shugabancin 2023

Gwamna El-Rufai Ya Bayyana Abinda Ya Kamata Yankin Kudu Maso Gabas Ya Yi Don Lashe Shugabancin 2023

- Gwamna Nasir El-Rufai ya mayar da martani ga kudirin takarar shugaban kasa na yankin kudu maso gabas

- El-Rufai yayi tir da yadda 'yan kabilar Igbo ke neman shugabancin kasar

- Dan siyasar ya bada shawarwari kan yadda mutanen kudu maso gabas zasu iya samun kujerar shugaban kasa

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shawarci yankin kudu maso gabas da su nemi takarar shugaban kasa ta hanyar siyasa, maimakon yin barazanar.

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, El-Rufai ya bayar da wannan shawarar ne a ranar Laraba, 6 ga watan Mayu, a wani taro ta shafin yanar gizo da kungiyar Shugabancin Afirka ta shirya.

KU KARANTA KUMA: Abubuwa 7 da ya kamata ku sani game da marigayiya Aisha Alhassan, Mama Taraba

Gwamna El-Rufai Ya Bayyana Abinda Ya Kamata Yankin Kudu Maso Gabas Ya Yi Don Lashe Shugabancin 2023
Gwamna El-Rufai Ya Bayyana Abinda Ya Kamata Yankin Kudu Maso Gabas Ya Yi Don Lashe Shugabancin 2023 Hoto: @elrufai
Asali: Facebook

Gwamnan ya bayyana cewa siyasa tana da alaƙa da tattaunawa da shawo kan wasu don su zaɓe ku.

Ya ce:

‘’Bana jin tunani akwai wani wanda ya hana Kudu maso Gabas neman Shugabancin kasar. Amma kun gani, ba za ku iya samun Shugabancin Najeriya ta hanyar barazanar ko ihu da cin mutunci ba. Wannan tsarin siyasa ne kuma dole ne ka nemi wasu bangarorin na Najeriya domin ka shawo kansu su mara maka baya.''

PM News ta ruwaito cewa El-Rufai bai yarda da tsarin da kudu maso gabas ke bi ba wajen neman shugabancin kasar, yana mai cewa barazanar ballewa ba zai amfanar da bukatun yankin ba.

KU KARANTA KUMA: Matasan Najeriya 5 da suka daukaka martabar kasar a idon duniya, karamin cikinsu shekararsa 10

Ya ce:

Fadar shugaban kasa ba ta hanyar kasaftawa ba ne. Sakamakon tsarin siyasa ne. Ku shiga kungiyar siyasa, kungiyar ku ta tattauna da sauran sassan kasar kuma hakan ta faru. Haka akeyi. Kuma ba za ku iya samun sa ta hanyar zama ko barazanar ballewa ba. Ba zai yi aiki ba.''

A wani labarin, da yawa daga cikin masu amfani da kafafen sadarwa sun caccaki gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai bayan ya bukaci a tarwatsa yan bindigar da suka yi garkuwa da dalibai 29 na Kwalejin Gandun Daji, Afaka, ko da kuwa haka zai janyo wasu dalibansu rasa ransu.

El-Rufai a wata tattaunawar yanar gizo da shugabannin Africa suka shirya karkashin Pastor Ituah Ighodalo, ranar Alhamis, ya ce gwamnatin jihar a shirye take ta hakura da rayuwar daliban a kokarin murkushe yan bindigar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel