Da duminsa: 'Yan bindiga sun sake kwashe daliban jami'a da ba a san yawansu ba
- Miyagun 'yan bindiga sun sace daliban jami'ar jihar Abia dake Uturu a daren Laraba
- 'Yan bindigan sun kwashe daliban da ba a san yawansu ba bayan tare su da suka yi a titi
- Gwamnatin jihar ABia tace ta hada kai da ta Imo wurin tabbatar da ta ceto daliban
Wasu 'yan bindiga dauke da miyagun makamai sun sace daliban jami'ar jihar Abia dake Uturu (ABSU).
Kamar yadda rahotanni suka bayyana, lamarin ya auku ne a cikin dare Laraba inda 'yan bindigan suka tsare wata motar haya dauke da daliban dake dawowa daga Okigwe zuwa Uturu wurin karfe 8.
Kamar yadda Vanguard ta wallafa, gwamnatin jihar Abia tace ta tsananta kokari wurin tabbatar da dawowar daliban da aka sace.
Kwamishinan yada labarai na jihar, Cheif John Okiyi Kalu, wanda ya bada wannan tabbacin ga manema labarai, yace gwamnatin jihar ta hada kai da jihar Imo mai makwabtaka domin ceto daliban.
KU KARANTA: Nasara daga Allah: Sojin saman Najeriya sun ragargaji 'yan bindiga a yankunan Kaduna
KU KARANTA: Da duminsa: Mabiyan Father Mbaka sun fito zanga-zanga bayan bacewarsa a Enugu
Kamar yadda takardar ta bayyana: "Gwamnatin jihar Abia tana lura da wani lamari da ya faru a Okigwe, jihar Imo. 'Yan bindiga sun sace daliban jami'ar jihar Abia a kan babbar hanyar Okigwe zuwa Uturu.
"Binciken farko ya nuna cewa an kwashe daliban ne a wata mota wurin karfe 7 zuwa 8 na yamma kuma an shigar dasu daji. Biyu daga cikin daliban sun yi nasarar tserowa amma sauran na hannun miyagun.
"Gwamnatin jihar Abia ta hada kai da ta Imo domin ganin ta ceto daliban. Gwamnatin Abia na tabbatar da cewa ba za ta bar wani dan ta'adda ya shakata ba domin hakkinta ne kare rayukan jama'arta da baki."
A wani labari na daban, mai digirin digirgir, Dr Auwal Mustapha Imam, wanda kwamitin tantancewa na jam'iyyar APC a jihar Kaduna suka hana takarar kujerar shugabancin karamar hukuma, ya koka akan abinda ya faru.
Imam yana daya daga cikin daruruwan 'yan takarar da aka sa suka rubuta jarabawa tare da tantancesu karkashin kwamitin tantancewa kafin zuwan zaben fidda gwani a jihar Kaduna.
Kamar yadda ya sanar da Legit.ng, "Kwamitin tantance ƴan takara sun yi batanci gareni ta hanyar lakaba min cewa ba na biyayya ga jam'iyya."
Asali: Legit.ng