Da duminsa: Shahararren malamin Musulunci ya yi rashi na matarsa
- An jefa jihar Kwara cikin jimami sakamakon mutuwar matar babban limamin masarautar Ilorin, Hajiya Hafsat Bashir Imam
- Tsohon shugaban majalisar dattijan Najeriya, Bukola Saraki, ya mika ta’aziyyarsa ga babban limamin tare da dangin duka
- Saraki a sakon ta’aziyar sa ya jinjina wa marigayiyar, inda ya bayyana ta a matsayin ginshikin tallafi ga mijinta da ‘ya’yanta
Hajiya Hafsat Bashir Imam, matar Sheikh Muhammadu Bashir Soliu, babban limamin masarautar Ilorin ta rasu.
An sanar da mutuwar ta ne a ranar Juma’a, 7 ga watan Mayu, ta hanyar sakon ta’aziyya da tsohon shugaban majalisar dattijan Najeriya kuma tsohon gwamnan jihar Kwara, Bukola Saraki ya wallafa a shafinsa na Twitter.
KU KARANTA KUMA: Gwamna El-Rufai Ya Bayyana Abinda Ya Kamata Yankin Kudu Maso Gabas Ya Yi Don Lashe Shugabancin 2023
Yayin da yake mika ta'aziyarsa ga babban limamin, Saraki ya bayyana cewa za a ci gaba da tunawa da marigayiyar a matsayin mace mai tsoron Allah kuma ginshiƙin tallafawa mijinta da 'ya'yanta.
Ya yi addu'a ga Allah da ya ba Hajiya Hafsat Aljannah Firdaus kuma ya ba wa iyalanta haƙurin jure rashin.
Ya wallafa:
"Ni da iyalina muna yin ta'aziyya ga Babban Limamin Masarautar Ilorin, Sheikh Muhammadu Bashir Soliu, bisa rasuwar matarsa, Hajiya Hafsat Bashir Imam.
"Zamu ci gaba da tunawa da Hajiya Hafsat a matsayinta na mace mai tsoron Allah kuma ginshiki na tallafi ga mijinta da 'ya'yanta.
"Za a yi kewar Hajiya Hafsat sosai saboda sadaukarwar da ta yi wa iyalai da kuma al’umman gari.
"Allah Ya ba ta matsayi a cikin salihai a cikin Aljannah firdaus kuma Ya ba wa iyalinta ƙarfin jure rashin."
A wani labarin kuma, tsohon mataimakin Shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya nuna alhini a kan mutuwar tsohuwar ministar harkokin mata, Aisha Alhassan Jummai.
KU KARANTA KUMA: An Bankado Manyan Mutanen Dake Daukar Nauyin Ta’addanci a Najeriya – Malami
Aisha wacce aka fi sani da suna Mama Taraba, ta rasu a ranar Juma’a, 7 ga watan Mayu, a Alkahira, Masar.
Atiku ya bayyana marigayiyar a matsayin mace mai tausayi da biyayya da burin ganin an samu Najeriya mai inganci.
Asali: Legit.ng