Na Kaɗu Matuƙa Da Samun Labarin Mutuwar Aisha Alhassan, Atiku

Na Kaɗu Matuƙa Da Samun Labarin Mutuwar Aisha Alhassan, Atiku

- Alhaji Atiku Abubakar, tsohon mataimakin Shugaban kasa ya yi alhinin mutuwar Aisha Alhassan Jummai

- Atiku ya bayyana marigayiyar tsohuwar ministar a matsayin mace mai kirki da kishin kasa

- Ya kuma mata addu'ar samun Aljannatul Firdausi

Tsohon mataimakin Shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya nuna alhini a kan mutuwar tsohuwar ministar harkokin mata, Aisha Alhassan Jummai.

Aisha wacce aka fi sani da suna Mama Taraba, ta rasu a ranar Juma’a, 7 ga watan Mayu, a Alkahira, Masar.

KU KARANTA KUMA: An Bankado Manyan Mutanen Dake Daukar Nauyin Ta’addanci a Najeriya – Malami

Na Kaɗu Matuƙa Da Samun Labarin Mutuwar Aisha Alhassan, Atiku
Na Kaɗu Matuƙa Da Samun Labarin Mutuwar Aisha Alhassan, Atiku Hoto: @SenAishaAlhassn
Asali: Twitter

Atiku ya bayyana marigayiyar a matsayin mace mai tausayi da biyayya da burin ganin an samu Najeriya mai inganci.

A wasu jerin wallafa da yayi a shafinsa na Twitter, dan takarar na shugaban kasa na jjam'iyyar PDP a zaben 2019, ya kuma yi mata addu'ar samun dacewa a cikin wannan wata mai tsarki.

Ya ce:

"Na kaɗu mutuka da samun labarin rasuwar tsohuwar ministar harkokin mata Sanata Aisha Al-Hassan, ko a yau din nan da rana na tambayi yanayin jikin ta, bayan na kira wayarta ba a "dauka ba. Innalillahi wa ina ilaihirraji'un!

"Allah Ya gafarta mata zunubanta Ya bata Aljannar Fiddausi cikin wannan wata Mai girma.

"Maman Taraba kamar yadda aka fi sanin ta, ta kasance tsayayyiyar ƴar siyasa kuma ma'aikaciyar Gwamnati mai kishin ƙasa.

"Mace ce mai tausayi da biyayya mai ƙudirin ganin an samar da Najeriya abar alfahari.

KU KARANTA KUMA: Abubuwa 7 da ya kamata ku sani game da marigayiya Aisha Alhassan, Mama Taraba

"Tabbas an yi babban rashi, haƙiƙa na yi rashin ƴar uwa kuma amintacciya ta."

A baya mun kawo cewa Allah ya yi wa tsohuwar ministan harkokin mata, Sanata Aisha Alhassan rasuwa.

Aisha Alhassan wacce aka fi sani da Mama Taraba ta rasu ne a wani asibiti a kasar waje.

Mama Taraba ta rasu ne bayan ta dade tana fama da rashin lafiya a karshen rayuwarta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel