Abubuwa 7 da ya kamata ku sani game da marigayiya Aisha Alhassan, Mama Taraba
Tsohuwar Ministar Harkokin Mata, Aisha Jummai Al-Hassan da ake kira Mama Taraba ta rasu tana da shekaru 61.
An tattaro cewa ta mutu a ranar Juma'a, 7 ga watan Mayu a Alkahira, Masar.
Ga abubuwa bakwai da ya kamata a sani game da marigayiyar:
1. Aisha Jummai Al-Hassan wacce aka fi sani da ‘Mama Taraba’, an haife ta a ranar 16 ga watan Satumba, 1959 a Jalingo, Jihar Taraba.
KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: IPOB ta sha mummunan kaye yayin da Sojojin Najeriya suka kashe mayaƙan kungiyar 11
2. Ita ce mace ta farko da aka nada a matsayin Atoni Janar kuma Kwamishinar Shari’a ta Taraba sannan kuma mace ta farko da aka nada a matsayin Sakatariyar Babban Kotun Shari’a ta FCT a ranar 17 ga watan Disambar 2003.
3. An bata mukami a shekarar 2015 a cikin majalisar ministocin Shugaba Muhammadu Buhari bayan zaben sa.
4. Mama Taraba ta yi murabus daga mukamin ta na Minista a ranar 27 ga watan Yuli, 2018 bayan kwamitin tantancewa na jam’iyyar APC mai mulki ya dakatar da ita daga zaben fitar da gwani na kujerar gwamna a shekarar 2019.
5. An bayyana ta a matsayin ‘yar takarar zaben gwamnan jihar Taraba karkashin jam’iyyar UDP a watan Maris na 2019, bayan daya yar takarar ta janye kudirinta na neman kujerar.
KU KARANTA KUMA: Matasan Najeriya 5 da suka daukaka martabar kasar a idon duniya, karamin cikinsu shekararsa 10
6. An fi saninta da suna 'Mama Taraba', saboda karin tasirin da take da shi a siyasar jiharta.
7. Ta himmatu wajen tallafawa kungiyar Kwallon kafa ta jihar Taraba.
A baya mun kawo cewa, Sanata Aisha Alhassan, tsohuwar ministan Harkokin Mata da aka fi sani da Mama Taraba ta rasu.
Daily Trust ta ruwaito cewa marigayiyar ta rasu ne a wani asibiti a kasar waje amma a halin yanzu babu cikaken bayani kan abin da ya yi sanadin rasuwarta.
Asali: Legit.ng