El-Rufai Ya Sha Zafafan Martani Don Kalamansa Kan Ceto Ɗaliban Afaka
- Kalaman Gwamna Nasir El-Rufai sun janyo zazzafar muhawara a shafukan sada zumunta
- Gwamnan ya bayyana cewa za su murkushe yan bindiga ko da wanda suka yi garkuwa da su za su rasa ransu
- An samu mabanbantan ra'ayi, yayin da wasu ke ganin ya yi dai dai, wasu kuma sabanin haka
Da yawa daga cikin masu amfani da kafafen sadarwa sun caccaki gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai bayan ya bukaci a tarwatsa yan bindigar da suka yi garkuwa da dalibai 29 na Kwalejin Gandun Daji, Afaka, ko da kuwa haka zai janyo wasu dalibansu rasa ransu.
El-Rufai a wata tattaunawar yanar gizo da shugabannin Africa suka shirya karkashin Pastor Ituah Ighodalo, ranar Alhamis, ya ce gwamnatin jihar a shirye take ta hakura da rayuwar daliban a kokarin murkushe yan bindigar.
DUBA WANNAN: Mutanen Gari Sun Ƙona Ƴan Bindiga Uku Ciki Har da Mace a Sokoto
Ya ce, "mun sani akwai hadari, mun san a garin haka zamu iya rasa rayukan wanda aka sace amma ya za muyi, dole haka zamu yi."
Wannan maganar ta janyo cecekuce da janyo hankalin masu amfani da kafafen sada zumunta.
Yusuf Angye a shafin sa na Facebook ya bada shawara cewa "a tuntubi masu basira da gogewa a irin wannan harka kada iyaye su ga rayuwar yayan su tazo karshe".
Mython Chijioke ya bayyana cewa bai kamata gwamnan ya yi wannan furuci ga al'umma ba, "koda hakan za ayi, ba komai ya kamata a bayyanawa mutane ba."
Hajjabintu Babashehu cewa tayi, "yanzu da aka saki daliban, kai da sojojin ka sai ku je ku murkushe su don hana faruwar haka nan gaba tunda kunsan inda suke, shikenan.
KU KARANTA: Da Ɗumi-Ɗumi: An Hana Hawa Dawakai Yayin Bukukuwa da Shagulgula a Niger
Sai dai, wasu daga cikin sun na neman ba'asin kalaman sa.
@realchado a Twitter, ya yadda da gwamnan kamar yadda ya wallafa, "duk da munin hakan, ina jin yafi da ace an biya kudin fansa.
"Zai magance wannan mummunar matsala in dai gwamnati ta maida hankali akan haka."
A wani labarin daban tsohon mataimakin shugaban kasa Mr Atiku Abubakar, a ranar Litinin, ya zargi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da musgunawa kafafen watsa labarai da yi wa yan kasa barazana idan sun bayyana ra'ayoyinsu.
Atiku ya yi wannan zargin ne cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter @atiku domin bikin ranar Yan Jarida na Duniya.
Ya bayyana cewa idan ana tauye hakkin mutane a mulkin demokradiyya, hakan zai kawo rashin jituwa tsakanin mutane da gwamnatin kasa.
Asali: Legit.ng