Mun Yafe Wa Ƴan Bindigan Da Suka Yi Garkuwa Da Mu, Ɗaliban Afaka

Mun Yafe Wa Ƴan Bindigan Da Suka Yi Garkuwa Da Mu, Ɗaliban Afaka

- Daliban kwallejin tarayya na nazarin gandun daji, Afaka da ke Kaduna sun ce sun yafewa yan bindiga

- Sarah Sunday, wacce ta yi magana a madadin daliban ta ce sun sha bakar wahala a hannunsu amma suna musu fatar shiriya

- Sarah ta yi wannan jawabin ne a ranar Juma'a a yayin da gwamnati ta sada daliban da iyalansu bayan likitoci sun duba su

Sarah Sunday, ɗaya daga cikin ɗaliban Kwalejin Nazarin Gandun Daji, Afaka a Kaduna ta ce sun yafewa waɗanda suka sace su, The Cable ta ruwaito.

An sace ɗaliban ne a lokacin da ƴan bindiga suka kai hari a makarantarsu a ranar 12 ga watan Maris na 2021.

Mun Yafewa Ƴan Bindigan Da Suka Yi Garkuwa Da Mu, Ɗaliban Afaka
Mun Yafewa Ƴan Bindigan Da Suka Yi Garkuwa Da Mu, Ɗaliban Afaka. Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

Yan bindiga sun sace ɗaliban ne a ranar 12 ga watan Maris na shekarar 2021. Duk da cewa su 39 aka sace yayin harin, an sako 10 daga cikinsu a baya.

Amma sauran daliban ba a sako su ba har sai ranar Laraba - bayan tsare su na makonni bakwai.

Gwamnatin jihar Kaduna ta garzaya da ɗaliban zuwa asibiti ne domin a duba lafiyarsu kafin daga bisani a yau Juma'a aka sada su da iyalansu.

DUBA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Aisha Alhassan, Mama Taraba, Ta Riga Mu Gidan Gaskiya

Da ta ke magana da manema labarai bayan an sada su da yan uwansu a ranar Juma'a, Sarah ta ce sun sha baƙar wahala a hannun waɗanda suka sace su tana mai cewa sunyi tafiya a kasa mai tsawo sosai.

Ta ce ta shiga damuwa kan lafiyar mahaifiyarta sakamakon sace su da aka yi kuma ta godewa dukkan wadanda suka taimaka don ganin an sako su.

"Zan fada musu (tana nufin masu garkuwar) cewa dukkanin mu mun yafe musu. Shi ke nan. Wannan shine kaɗai abin da zan faɗa musu. Kuma Allah zai ba su ikon su canja halayensu," in ji ta.

"Mun sha baƙar wahala. Maganan gaskiya mun sha zagi, da ayyuka masu wahala. Munyi tafiya a ƙasa har mun gaji.

KU KARANTA: Rashin Tsaro: Jam'iyyar APC Ta Roƙi Ƴan Nigeria Su Marawa Buhari Baya

"Na yi tunanin mahaifiyata za ta mutu saboda firgici amma na godewa Allah. Nagode. Mun godewa kowa da ya taimake mu da addu'a da komai."

A wani labarin daban tsohon mataimakin shugaban kasa Mr Atiku Abubakar, a ranar Litinin, ya zargi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da musgunawa kafafen watsa labarai da yi wa yan kasa barazana idan sun bayyana ra'ayoyinsu.

Atiku ya yi wannan zargin ne cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter @atiku domin bikin ranar Yan Jarida na Duniya.

Ya bayyana cewa idan ana tauye hakkin mutane a mulkin demokradiyya, hakan zai kawo rashin jituwa tsakanin mutane da gwamnatin kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel