Rashin Tsaro: Jam'iyyar APC Ta Roƙi Ƴan Nigeria Su Marawa Buhari Baya

Rashin Tsaro: Jam'iyyar APC Ta Roƙi Ƴan Nigeria Su Marawa Buhari Baya

- Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ta roƙi ƴan Nigeria su cigaba da goyon bayan Shugaba Muhammadu Buhari

- Jam'iyyar mai mulki ta yi wannan roƙon ne cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis na murnar sako ɗaliban Afaka 29

- Sakataren jam'iyyar APC na ƙasa ya ce suma sun damu da halin rashin tsaro da kasar ke ciki amma akwai bukatar a marawa Buhari baya a yayin da ya ke kokarin magance matsalar

Jam'iyyar All Progressives Congress ta roƙi ƴan Nigeria su goyi bayan Shugaba Muhammadu Buhari a yayin da ya ke ƙoƙarin kawo ƙarshen ƙallubalen tsaro da ke addabar ƙasar, rahoton The Punch.

Wannan roƙon na cikin sanarwar ce mai taken 'APC na maraba da sako ɗaliban kwalejin Kaduna su 29', mai ɗauke da sa hannun sakataren jam'iyyar na ƙasa Senata John Akpanudoeudehe a Abuja a ranar Alhamis.

Rashin Tsaro: Jam'iyyar APC Ta Roƙi Ƴan Nigeria Su Marawa Buhari Baya
Rashin Tsaro: Jam'iyyar APC Ta Roƙi Ƴan Nigeria Su Marawa Buhari Baya. Hoto: @MobilePunch

DUBA WANNAN: 'Yan Bindiga Sun Kashe Ɗan Jarida, Sunyi Garkuwa da Matafiya da Dama a Katsina

A cewarsa, jam'iyyar ta APC ta yi murnar ganin an sako ɗaliban 29 da aka sace daga Kwalejin Tarayya ta Nazarin Gandun Daji da ke Afaka a Jihar Kaduna.

Ya ce, "Abin farin ciki ne ganin yadda aka sada ɗaliban da iyalansu, abokai da sauran masoyansu. Muna miƙa godiya da dukkan masu ruwa da tsaki da suka taimaka aka sako ɗaliban.

KU KARANTA: Gumi Ya Faɗa Mana Gaskiya, Yana Tare Da Ƴan Ta’adda Ne Ko Ƴan Nigeria, Adamu Garba

"Yayin da jam'iyyar da gwamnati ke damuwa kan halin rashin tsaro a sassan kasar kamar sauran mutane, muna kira ga ƴan Nigeria su cigaba da goyon bayan ƙoƙarin da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ke yi domin samar da mafita na dindindin cikin gaggawa."

A wani labarin daban tsohon mataimakin shugaban kasa Mr Atiku Abubakar, a ranar Litinin, ya zargi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da musgunawa kafafen watsa labarai da yi wa yan kasa barazana idan sun bayyana ra'ayoyinsu.

Atiku ya yi wannan zargin ne cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter @atiku domin bikin ranar Yan Jarida na Duniya.

Ya bayyana cewa idan ana tauye hakkin mutane a mulkin demokradiyya, hakan zai kawo rashin jituwa tsakanin mutane da gwamnatin kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel