Yanzu-Yanzu: Aisha Alhassan, Mama Taraba, Ta Riga Mu Gidan Gaskiya

Yanzu-Yanzu: Aisha Alhassan, Mama Taraba, Ta Riga Mu Gidan Gaskiya

- Allah ya yi wa tsohuwar ministan harkokin mata, Sanata Aisha Alhassan rasuwa

- Aisha Alhassan wacce aka fi sani da Mama Taraba ta rasu ne a wani asibiti a kasar waje

- Mama Taraba ta rasu ne bayan ta dade tana fama da rashin lafiya a karshen rayuwarta

Sanata Aisha Alhassan, tsohuwar ministan Harkokin Mata da aka fi sani da Mama Taraba ta rasu.

Daily Trust ta ruwaito cewa marigayiyar ta rasu ne a wani asibiti a kasar waje amma a halin yanzu babu cikaken bayani kan abin da ya yi sanadin rasuwarta.

Yanzu-Yanzu: Aisha Alhassan, Mama Taraba, Ta Riga Mu Gidan Gaskiya
Yanzu-Yanzu: Aisha Alhassan, Mama Taraba, Ta Riga Mu Gidan Gaskiya
Asali: Original

Marigayiyar ta yi fama da rashin lafiya a shekarunta na karshe a duniya.

Alhassan ta yi takarar gwamnan jihar Taraba a 2015 a karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) amma ta sha kaye a hannun gwamna mai ci a wancan lokacin Darius Ishaku wanda ya yi takara a karkashin jam'iyyar PDP.

DUBA WANNAN: Mutanen Gari Sun Ƙona Ƴan Bindiga Uku Ciki Har da Mace a Sokoto

Jim kadan bayan ta sha kaye a zaben, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada ta matsayin Ministan Harkokin Mata.

Sai dai daga bisani ta bar aiki cikin wani yanayi mai daure kai bayan jam'iyyar APC ta gaza tantance ta domin takarar kujerar gwamna a zaben 2019.

Hakan yasa ta yi murabus daga kujerarta da sauya sheka zuwa jam'iyyar United Democratic Party (UDP).

Alhassan ta fara fuskantar matsaloli ne a jam'iyyar APC karkashin shugabancin Adams Oshiomhole a lokacin da ta goyi bayan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar gabanin babban zaben 2019.

KU KARANTA: Gumi Ya Faɗa Mana Gaskiya, Yana Tare Da Ƴan Ta’adda Ne Ko Ƴan Nigeria, Adamu Garba

Goyon bayan Atikun da ta yi ya sosawa shugaban jam'iyyar na APC rai domin ba a tsammanin minista da ke aiki da gwamnatin APC ta bayyana goyon bayanta ga dan jam'iyyar hamayya wato PDP.

Daga bisani Atiku Abubakar ya samu tikitin takarar amma ya sha kaye a babban zabe.

A wani labarin daban tsohon mataimakin shugaban kasa Mr Atiku Abubakar, a ranar Litinin, ya zargi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da musgunawa kafafen watsa labarai da yi wa yan kasa barazana idan sun bayyana ra'ayoyinsu.

Atiku ya yi wannan zargin ne cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter @atiku domin bikin ranar Yan Jarida na Duniya.

Ya bayyana cewa idan ana tauye hakkin mutane a mulkin demokradiyya, hakan zai kawo rashin jituwa tsakanin mutane da gwamnatin kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel