Gara mu rasa rayukanmu da a tsige Buhari daga kujerarsa, Masoyan shugaban kasa

Gara mu rasa rayukanmu da a tsige Buhari daga kujerarsa, Masoyan shugaban kasa

- Kungiyar #IstandwithBuhari# ta tabbatar da cewa babu wasu miyagu da suka isa su tsige shugaban kasa daga kujerarsa kafin 2023

- Kungiyar ta mutum miliyan 25 ta ce da a tsige shugaban kasa Buhari daga kujerarsa gara dukkansu su rasa rayukansu

- Kamar yadda shugaban kungiyar, Ifeanyi Nonso ya tabbatar, yace zasu baiwa mulkin Buhari kariya da digon karshen jininsu

Wata kungiyar karkashin inuwar #IstandwithBuhari# tace shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai saurari miyagun da ke kira gareshi ba da ya sauka mulki kafin cikan wa'adin mulkinsa a 2023.

A yayin jawabi ga manema labari a ranar Alhamis a cibiyar Yar'adua dake Abuja, shugaban kungiyar mai suna Ifeanyi Nonso, wanda ya samu goyon bayan sauran 'yan kungiyar, ya ce wasu 'yan siyasa ne a kasar nan ke daukar nauyin kashe-kashe.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, ya ce wasu 'yan siyasa ne a kasar nan ke zagon kasa ga kokarin gwamnati na shawo kan matsalar tsaro da ta addabi kasar nan inda ya kara da cewa nan babu dadewa asirinsu zai tonu.

KU KARANTA: Da duminsa: Gwamnatin tarayya ta amince da fara amfani da fasahar 5G

Gara mu rasa rayukanmu da a tsige Buhari daga kujerarsa, Masoyan shugaban kasa
Gara mu rasa rayukanmu da a tsige Buhari daga kujerarsa, Masoyan shugaban kasa. Hoto daga @daily_trust
Asali: UGC

KU KARANTA: Gumi: Ban san komai a kan N800,000 da aka karba ba domin sako daliban Afaka

"Akwai matukar amfani mu sanar da cewa babu shakka ba za a iya yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari barazana ba ko wani abinda zai sa ya bar mulki har sai 2023.

"Duk wani mutum ko kungiya, ko waye, wanda ya yadda zai iya amfani da ta'addanci wajen ganin bayan Buhari, ya sani cewa yana mu'amala ne da mutum miliyan 25 da suka zabi shugaban kasa kuma zasu iya rasa rayukansu a kan su ga wani mugun abu ya faru da mulkinsa.

“Abinda ke faruwa a Najeriya a yau mutum ne ke shiryawa saboda son kai da kuma kokarin tarwatsa kasar.

“Kungiyar mu na so nsanar da su cewa kasar nan ba zata rabu ba kuma babu abinda za a iya mata ta rabu. Zamu bata kariya da digon karshe na jininmu," yace.

A wani labari na daban, mai digirin digirgir, Dr Auwal Mustapha Imam, wanda kwamitin tantancewa na jam'iyyar APC a jihar Kaduna suka hana takarar kujerar shugabancin karamar hukuma, ya koka akan abinda ya faru.

Imam yana daya daga cikin daruruwan 'yan takarar da aka sa suka rubuta jarabawa tare da tantancesu karkashin kwamitin tantancewa kafin zuwan zaben fidda gwani a jihar Kaduna.

Kamar yadda ya sanar da Legit.ng, "Kwamitin tantance ƴan takara sun yi batanci gareni ta hanyar lakaba min cewa ba na biyayya ga jam'iyya."

Asali: Legit.ng

Online view pixel