Tsagerun IPOB sun kone ofishin 'yan sanda, sun sheke jami'ai 2 a Anambra

Tsagerun IPOB sun kone ofishin 'yan sanda, sun sheke jami'ai 2 a Anambra

- Bayan nada sabon kwamishinan 'yan sanda a jihar Anambra, tsagerun IPOB sun kone ofishin 'yan sanda

- 'Yan bindigan sun bankawa ofishin 'yan sandan wuta tare da sheke wasu jami'ai biyu a Obosi dake Idemili

- Kwamishinan 'yan sandan jihar ya tura jami'ai inda abun ya faru sannan an kwashe gawawwakin wadanda suka rasu

Kasa da sa'o'i 24 da nada sabon kwamishinan 'yan sanda a jihar Anambra, Christopher Adetokumbo Owolabi, 'yan bindiga sun kai farmaki ofishin 'yan sanda dake Obosi a karamar hukumar Idemili a jihar inda suka sheke 'yan sanda biyu.

'Yan bindigan sun kai farmaki ofishin 'yan sandan a yammacin Laraba inda suka saki dukkan masu laifi dake ofishin sannan suka banka masa wuta, Daily Trust ta wallafa.

Wata majiya mai kusanci da ofishin 'yan sandan tace 'yan bindiga sun isa da yawansu kuma sun kai hari ofishin wurin karfe 11 na dare. Ya bayyana sunayen jami'an da Sifeta James da Awalu.

KU KARANTA: Nasara daga Allah: Sojin saman Najeriya sun ragargaji 'yan bindiga a yankunan Kaduna

Tsagerun IPOB sun kone ofishin 'yan sanda, sun sheke jami'ai 2 a Anambra
Tsagerun IPOB sun kone ofishin 'yan sanda, sun sheke jami'ai 2 a Anambra. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Mabiyan Father Mbaka sun fito zanga-zanga bayan bacewarsa a Enugu

Majiyar tace wadanda abun ya shafa aka kashe su ne a wani gidan mai kusa da ofishin 'yan sandan.

Majiyar tace yayin da 'yan sandan ke kan aikinsu, sun gane cewa akwai 'yan bindiga dake kaiwa da kawowa, lamarin da yasa suka fara gudu.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Anambra ya tabbatar da kisan jami'an har biyu.

DSP Tochukwu Ikenga, kakakin rundunar 'yan sandan, wanda ya tabbatar da harin, yace kwamishinan 'yan sandan jihar ya tura jami'ai domin duba yadda lamarin yake.

Ikenga ya kara da cewa an mika gawawwakin 'yan sandan ma'adanar gawawwaki kuma ana cigaba da bincike.

A wani labari na daban, Ahmad Gumi, fitaccen Malamin addinin Islama, ya musanta sanin komai a kan N800,000 da aka biya domin a sako daliban makarantar Afaka da aka sace a jihar Kaduna.

A watan Maris ne 'yan bindiga suka kai hari kwalejin gandun daji dake Afaka a karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna suka sace dalibai 39.

Amma kuma tuni aka sako 10 daga cikin daliban inda guda 29 aka sako su a ranar Laraba, 5 ga watan Mayu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel