Mazauna da Masu Shaguna Sun Tsere Yayin Da Tankar Mai Ta Fadi a Abuja

Mazauna da Masu Shaguna Sun Tsere Yayin Da Tankar Mai Ta Fadi a Abuja

- Wata babbar mota ta yi hatsari a wani yankin Abuja, an yi asarar man fetur a yayin hatsarin

- Shaidun gani da ido sun bayyana, mazauna yankin sun tattara kayayyakinsu don neman tsira

- Hakazalika jami'an tsaro sun rufe hanyar da aka yi hatsarin don kula da dukiyoyin al'umma

Wata tankar dakon mai dauke da kayan da ake zargin man fetur ne, ta yi hatsari a kan babbar hanyar Mararaba zuwa Abuja da safiyar Talata.

An gano cewa man ya zube daga tankar da ta yi hatsari, yana kwarara ba kakkautawa zuwa shagunan da ke kusa da wuraren mazauna yankin.

Wannan ya jefa mazauna cikin rudani yayin da suka runtuma don kare lafiyarsu.

Wani ganau, wanda ya zanta da wakilin Daily Trust, ya ce a sakamakon hatsarin, wasu bata-gari sun yi amfani da damar wawushe kayayyaki daga shagunan da ba kowa.

Wani shaidar gani da ido, Hassan Abdulkareem, ya bayyana cewa tankar ta kubuce ne a kokarin kauce wa rami a babbar hanyar Mopol da ke Nyanya, wani yanki a cikin Babban Birnin Tarayya.

KU KARANTA: Iyayen Daliban da Aka Sace a Kaduna Sun Mamaye Bakin Majalisar Tarayya Dake Abuja

Mazauna da Masu Shaguna Sun Tsere Yayin Da Tankar Mai Ta Fadi a Abuja
Mazauna da Masu Shaguna Sun Tsere Yayin Da Tankar Mai Ta Fadi a Abuja Hoto: aljazirahnews.com
Asali: UGC

Ya ce: “Hatsarin ya faru ne a daren jiya [Litinin] kuma tankar tana dauke da PMS, sai kayan ya zube daga tankar zuwa shaguna da wuraren zama.

"Wannan ya sa da yawa daga cikin masu shaguna da kuma mazauna kusa da yankin, suka kwashe kayayyakinsu saboda tsoron barkewar gobara ba zato ba tsammani sakamakon barewar man," ya bayyana tsoronsa.

A cewarsa, lamarin da ya faru ya sanya jami'an tsaro toshe babbar hanyar, yayin da tuni jami'an hukumar kashe gobara daga Karu da Abuja suka halarci wajen don dakile duk wani abu da zai faru.

KU KARANTA: Boko Haram: Shekau Ya Sheke Wani Babban Kwandansa, Ya Nada Sabon Kwamanda

A wani labarin, Wani jirgin kasa mai dauke da bututun ruwa daga jihar Legas zuwa Zariya a jihar Kaduna ya yi hatsari a wani yankin jihar ta Kaduna.

Hatsarin wanda ya afku a yankin Unguwar Kanawa da ke Kaduna ya tilasta wa jirgin tashi daga layin dogo, wanda hakan ya sa biyar daga cikin taragon jirgin kaucewa daga kan hanyar.

Duk da cewa ba a samu asarar rayuka ba a lamarin, injiniyan da ke kula da ayyukan Arewa na kamfanin jirgin kasa na Najeriya, Haruna Ahmed ya shaida wa gidan talabijin na Channels cewa hatsarin jirgin ya faru ne sakamakon lalata hanyoyin jirgin da wasu bata-gari suka yi.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel