Rashin Tsaro: Babban Faston Najeriya Ya Bayyana Abun da Ya Gani Game da Juyin Mulkin Shugaba Buhari

Rashin Tsaro: Babban Faston Najeriya Ya Bayyana Abun da Ya Gani Game da Juyin Mulkin Shugaba Buhari

- Martani na ci gaba da bayyana game da ikirarin da fadar shugaban kasa ta yi cewa wasu ‘yan kasar na kulla makarkashiyar kifar da gwamnatin tarayya

- Primate Elijah Ayodele ya bayyana dalilin da ya sa juyin mulki ba zai yi nasara ba

- Shugaban addinin ya ba da shawarwari ga gwamnatin tarayya game da matsalolin Najeriya

Primate Elijah Ayodele, Shugaban Cocin INRI Evangelical Spiritual Church, ya bayyana cewa ba za a tsige Shugaba Muhammadu Buhari daga ofishin sa ba.

Ya ba da tabbacin cewa duk da cewa mulkin Buhari zai fuskanci cin hanci da rashawa, rudani, babu wani juyin mulki da za a yi mashi, PM News ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: FG Na Shirin Zabtare Albashin Ma’aikata Tare da Hade Hukumomi Don Rage Tsadar Gwamnati

Rashin Tsaro: Babban Faston Najeriya Ya Bayyana Abun da Ya Gani Game da Juyin Mulkin Shugaba Buhari
Rashin Tsaro: Babban Faston Najeriya Ya Bayyana Abun da Ya Gani Game da Juyin Mulkin Shugaba Buhari Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Martanin nasa ya biyo bayan gargadin da fadar shugaban kasa ta yi cewa wasu ‘yan kasar na shirin kwace gwamnatin tarayya.

A cewar Ayodele, Allah ya amince da dimokiradiyyar Najeriya don haka kokarin wargaza kasar zai ci tura.

Malamin ya ce duk da cewa gwamnatin za ta ci gaba da fuskantar rashin daidaito, matsin tattalin arziki, zanga-zanga, rashin tsaro, amma ba za a yi juyin mulki ba.

Faston ya gaya wa wadanda ke da hannu a cin amanar kasa su daina, ya kara da cewa ba Za su cimma nasara ba.

“Bai kamata Fadar Shugaban kasa ta ji tsoron kowane irin salon juyin mulki ba, ba za a yi juyin mulki ba. Babu wanda zai iya tumbuke gwamnatin duk da cewa mulkin zai kasance cikin rudani, lalacewa, da ruɗani.

“Yakamata fadar shugaban kasa su sanya kawunansu a matashi suyi baccinsu, babu wani juyin mulki da zai iya faruwa a Najeriya yanzu duk da cewa matsalar tattalin arziki, zanga-zanga, za ta ci gaba.

"Muddin gwamnati ta gaza yin aiki a kan rashin tsaro a kasar amma bai kamata su yi tunanin juyin mulki ba, ba zai cimma nasara ba.

“Allah ya fi mutane ƙarfi, ba na adawa da gwamnati amma na faɗi abin da Allah ya gaya mini, idan gwamnati ta ci gaba a haka, za a sami rashin daidaituwa sosai.

"Ba za su daidaita abubuwa ba sai sun saurari talakawa kuma sun magance matsalar da muke fuskanta."

KU KARANTA KUMA: Rashin Tsaro: Atiku Ya Ba da Mafita Don Yakar ’Yan Fashi da Masu Tayar da Kayar Baya

A halin yanzu, Ayodele ya kara da cewa gwamnati na bukatar sa hannun Allah don kawo karshen rashin tsaro a kasar.

A wani labarin, Shugaba Buhari ya nuna matuƙar rashin jin daɗinsa bisa wasu jerin hare-hare da yan bindiga suka kai jihohin Benuwai da Anambra.

Buhari yayi wannan jawabi ne a cikin wani saƙo da babban mai bashi shawara ta musamman kan harkokin yaɗa labarai, Garba Shehu, ya fitar.

Shugaban ya jajantawa waɗanda lamarin ya shafa, gwamnati da kuma al'ummar jihar baki ɗaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel