Buhari Yayi Allah Wadai da Sabon Harin da Wasu Yan Bindiga Suka Kai Benuwai, Ya Faɗi Matakin da Zai Ɗauka

Buhari Yayi Allah Wadai da Sabon Harin da Wasu Yan Bindiga Suka Kai Benuwai, Ya Faɗi Matakin da Zai Ɗauka

- Shugaba Buhari ya nuna matuƙar rashin jin daɗinsa bisa wasu jerin hare-hare da yan bindiga suka kai jihohin Benuwai da Anambra.

- Buhari yayi wannan jawabi ne a cikin wani saƙo da babban mai bashi shawara ta musamman kan harkokin yaɗa labarai, Garba Shehu, ya fitar

- Shugaban ya jajantawa waɗanda lamarin ya shafa, gwamnati da kuma al'ummar jihar baki ɗaya

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, a ranar Talatan nan yayi Allah wadai da kisan mutane 11 a ƙaramar hukumar Gwer ta yamma, jihar Benuwai, kamar yadda Punch ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Ban Taba Cewa Gwamnati Na Buga Kudi Ba Tun 2015, Amaechi

Wannan na ƙunshe ne a cikin wani jawabi da babban mai taimakawa shugaban na musamman kan yaɗa labarai, Malam Garba Shehu ya fitar, kuma aka yiwa take da 'Shugaba Buhari yayi Allah Wadai da duk wani tashin hankali, yace ba'a samun nasara dashi'

Buhari Yayi Allah Wadai da Sabon Harin da Wasu Yan Bindiga Suka Kai Benuwai, Ya Faɗi Matakin da Zai Ɗauka
Buhari Yayi Allah Wadai da Sabon Harin da Wasu Yan Bindiga Suka Kai Benuwai, Ya Faɗi Matakin da Zai Ɗauka Hoto: @MBuhari
Asali: Twitter

Jawabin shugaban yace: "Ina Allah wadai da wannan tashin hankalin da kuma harin da aka kaima mutanen da basu ji ba basu gani ba, waɗanda babu ruwansu da tashin hankali."

"Kai hari da kuma tayar da hankali ga mutanen da ba ruwansu ba abun yarda bane kuma ba zamu amince a cigaba da hakan ba."

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Wasu ’Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Shugaban Ƙungiyar Miyetti Allah

Hakanan shugaban ƙasan ya sake yin watsi da kisan da aka yiwa wasu mutane da babu ruwansu a Jihar Anambra wanda wasu yan bindiga suka yi.

Yace: "Idan muka bar wannan yanayin na tashe-tashen hankula ba tare da ɗaukar wani mataki ba, Yan bindiga zasu yi fata-fata da doka.

A jawabin, shugaban ƙasa ya roƙi shugabannin ƙabilu da na addinai da su sauke nauyin da aka ɗora musu wajen kula da mabiyansu.

Kuma su goyi bayan gwamnati a ƙoƙarin da take wajen dawo da dauwamammen zaman lafiya a faɗin ƙasar nan.

Daga ƙarshe shugaban yayi ta'aziyya ga iyalan waɗanda abun ya shafa, gwamnati da kuma mutanen jihohin Benuwai da Anambra baki dayan su.

A wani labarin kuma Ku Ƙara mana Lokaci kar ku kashe 'yayan mu, Iyayen Ɗalibai sun Roƙi yan Bindiga

Ƙungiyar iyaye malamai ta ƙasa NAPTAN ta yi kira ga yan bindigar da suka sace ɗaliban jami'ar Greenfield Kaduna da su ƙara bada lokaci domin tattaunawa.

Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Alhaji Haruna Ɗanjuma ne ya bayyana haka, yace bai kamata yan bindigan su rinka kashe waɗanda babu ruwansu ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel