FG Na Shirin Zabtare Albashin Ma’aikata Tare da Hade Hukumomi Don Rage Tsadar Gwamnati
- Gwamnatin tarayya na kokarin zabtare albashin ma'aikata tare da hade hukumomin da aikinsu ke kamanceceniya
- Kamar yadda ministan kudi, kasafi da tsari, Zainab Ahmed ta sanar, ta ce gwamnatin tarayya na kokarin rage yawan kudin da take kashewa
- Ta sanar da cewa shugaban kasa ne ya bata umarnin kuma tayi aiki tare da shugaban ma'aikata da kuma shugabannin hukumomin gwamnatin
A ranar Talata gwamnatin tarayya ta bukaci kwamitin albashi da ta sake duba tsarin albashi tare da zabge yawan hukumominta.
Ministan kudi, kasafi da tsari, Zainah Ahmed, ta bayyana hakan a garin Abuja a taron tattaunawa kan rashawa da rage yawan kudin da gwamnati ke kashewa a Najeriya, wanda hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta ta shirya.
Ta ce gwamnati ta amince da kasafin N13.88 tiriliyan tare da nakasun sama da N5.6 tiriliyan inda take tsammanin kudin shiga N7.98 tiriliyan wanda zata yi amfani dashi wurin daukan nauyin kasafin kudin.
KU KARANTA: Yan Boko Haram sun kutsa garinsu Zulum, sun sheƙe rayuka 7, sun kone gidaje
KU KARANTA: Da duminsa: An sheke wasu mutum 23 a sabon harin Binuwai
Kamar yadda tace: "Har a yanzu muna ganin cewa kudin da gwamnati za ta kashe ya ninka kudin shiganmu. Akwai bukatar mu yi aiki da hukumomin gwamnatin tarayya domin rage yawan kudin.
"Dole ne mu zabtare yawan kudin da zamu kashe kan abubuwa masu karancin amfani. Abubuwan da zamu iya zama babu su.
"Kasafinmu a cike yake a kowacce shekara ta yadda muke zama mu yi ta dubawa kuma muna saka abubuwan da ba dole bane a ciki.
"Shugaban kasa ya umarci kwamitin albashi da nake shugabanta, da mu yi aiki da shugaban ma'aikata tare da sauran mambobin kwamitin don duba albashi ta yadda zamu rage yawan kudin da gwamnati ke kashewa."
Ministan ta ce gwamnatin za ta sake duba yawan hukumomin da kuma amfaninsu inda tace hukumomin da ke da amfani kusan daya za a hade su.
A jawabinsa, shugaban hukumar ICPC, Farfesa Bolaji Owasanoye, ya ce yawan kudin da gwamnati ke kashewa shine tushen rashawa.
Ya ce mayar da hankalin gwamnati na duba tsarin albashi, cire tallafi da kuma zabtare yawan kudin da ake kashewa a kwangiloli duk suna daga cikin abubuwan da talaka zasu amfana dasu.
A wani labari na daban, hedkwatar tsaron Najeriya ta ja kunnen 'yan siyasa da manyan dakarun sojin kasar nan a kan shirya juyin mulki.
A wata takarda da hedkwatar tsaron ta fitar a ranar Litinin ta hannun Onyema Nwachukwu, mai magana da yawunta, yace hankalinsu ya kai kan wani tsokacin da Robert Clarke, babban lauya yayi na cewa a mika mulkin kasa ga soji.
Rundunar sojin ta tsame kanta daga wannan tsokacin kuma ta kwatanta shi da mai zagon kasa da damokaradiyya tare da cewa tana biyayya ga mulkin kasar nan, The Cable ta ruwaito.
Asali: Legit.ng