Rashin Tsaro: Atiku Ya Ba da Mafita Don Yakar ’Yan Fashi da Masu Tayar da Kayar Baya

Rashin Tsaro: Atiku Ya Ba da Mafita Don Yakar ’Yan Fashi da Masu Tayar da Kayar Baya

- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya koka da tabarbarewar yanayin tsaro a Najeriya

- Dan siyasar a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, 4 ga watan Mayu, ya bayar da shawarar samun mafita ga gwamnatin tarayya

- Tsohon dan takarar shugaban kasar ya bukaci gwamnati da ta dawo da dukkan tsoffin ma’aikata maza da mata don shiga yaki da rashin tsaro

An yi kira ga gwamnatin tarayya da ta sake dawo da hafsoshin soji maza da mata wadanda suka yi ritaya a matsayin mafita don magance matsalolin tsaro da ake fuskanta a kasar.

Legit.ng ta tattaro cewa tsohon mataimakin shugaban kasar, Atiku Abubakar ne ya bayar da wannan shawarar a cikin wata sanarwa da ya raba ta shafin sa na Facebook da Twitter a ranar Talata, 4 ga watan Mayu.

KU KARANTA: Bidiyon fasto tana yi wa 'yan cocinta tofin Allah tsine a kan sun ki tara mata kudin bikin bazday

Rashin Tsaro: Atiku Ya Ba da Mafita Don Yakar ’Yan Fashi da Masu Tayar da Kayar Baya
Rashin Tsaro: Atiku Ya Ba da Mafita Don Yakar ’Yan Fashi da Masu Tayar da Kayar Baya. Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

Atiku ya yi kira ga gwamnati da ta yi la’akari da sake dawo da wadanda ke da niyyar komawa bakin aiki, da kuma kai yaki ga maharan har sai anyi nasara a kansu.

Tsohon dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya bayyana cewa yanayin tsaro a Najeriya yana tabarbarewa cikin sauri, ya kara da cewa yanzu lokaci ne na jagoranci mai kyau.

Ya ci gaba da bayyana cewa lokaci ya yi da za mu sa himma sosai mu kawar da wannan barazanar daga kasarmu.

KU KARANTA: Yan Boko Haram sun kutsa garinsu Zulum, sun sheƙe rayuka 7, sun kone gidaje

A wani labari na daban, hedkwatar tsaron Najeriya ta ja kunnen 'yan siyasa da manyan dakarun sojin kasar nan a kan shirya juyin mulki.

A wata takarda da hedkwatar tsaron ta fitar a ranar Litinin ta hannun Onyema Nwachukwu, mai magana da yawunta, yace hankalinsu ya kai kan wani tsokacin da Robert Clarke, babban lauya yayi na cewa a mika mulkin kasa ga soji.

Rundunar sojin ta tsame kanta daga wannan tsokacin kuma ta kwatanta shi da mai zagon kasa da damokaradiyya tare da cewa tana biyayya ga mulkin kasar nan, The Cable ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng