Sanatan APC Ya Caccaki Mutanen Dake Kewaye da Buhari, Yace Babu Mai Iya Ɗaga Murya Don Kareshi

Sanatan APC Ya Caccaki Mutanen Dake Kewaye da Buhari, Yace Babu Mai Iya Ɗaga Murya Don Kareshi

- Sanata Rochas Okorocha yace shugaba Buhari yana bashi tausayi saboda shi kadai ne yake ƙoƙarin gyara ƙasar nan.

- Okorocha yace gaba ɗaya ministoci, daraktoci da dukkan na kusa da shugaban sun yi gum da bakinsu basa cewa komai wajen kare shugaban

- Sai-dai yayi kira ga matasa da su ƙara hakuri, Najeriya zata gyaru ta zama wata sabuwar ƙasa kuma matasa zasu walwala.

Tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ranar Talata yace shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, yana tsaye ne shi ɗaya a wajen dakile ƙalubalen tsaro da kuma karayar tattalin arziƙi da kasar nan ke fama dasu.

KARANTA ANAN: Ya Kamata CBN Ya Biya 100 Miliyan Na Fansar Ɗaliban Greenfield Tun Kafin Lokaci Ya Ƙure, Sheikh Gumi

Tsohon gwamnan yayi wannan jawabi ne yayin da wasu matasa suka kai masa ziyara daga jihar Cross Rivers a Babban birnin tarayya Abuja.

Okorocha yace babu wani da yake ɗaga murya yayi magana yana goyon bayan shugaba Buhari daga cikin waɗanda ya naɗa ko masu taimaka masa na musamman, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Sanatan APC Ya Caccaki Mutanen Dake Kewaye da Buhari, Yace Babu Mai Iya Ɗaga Murya Don Kare Shugaban
Sanatan APC Ya Caccaki Mutanen Dake Kewaye da Buhari, Yace Babu Mai Iya Ɗaga Murya Don Kare Shugaban Hoto: @RealRochas
Asali: Twitter

Okrochas Yace:

"Ina tausayawa shugaba Buhari a dai-dai wannan lokacin, domin komai na kanshi, ba wanda yake karesa ko yake taimaka masa, ministoci basa magana, daraktoci sun yi shiru, gaba ɗaya yan tawagarsa da yakamata suce Shugaban mu nayin wani abu duk sunyi shiru."

"Wannan itace matsalar mu, ita matsala dole ta faru, amma yadda za'a warwareta shine wani abu daban."

KARANTA ANAN: Buhari Yayi Allah Wadai da Sabon Harin da Wasu Yan Bindiga Suka Kai Benuwai, Ya Faɗi Matakin da Zai Ɗauka

Sanatan wanda yake wakiltar mazaɓar Imo ta yamma a majalisar dattijai, yayin da yake kira ga matasa su cigaba da ƙaunar Najeriya, yace matasa basa amfana da komai na gwamnatin APC.

A cewarsa: "Kar ku karaya da Najeriya, dole Najeriya ta gyaru, zata zama kamar sabuwar ƙasa, a wannan lokacin ne matasa Maza da mata zasu shana."

"Maganar gaskiya, ɓangaren jin dadi na jam'iyyar APC baya amfanar matasa da komai, kuma hakan na faruwa ne saboda fushin da muke gani a faɗin ƙasar."

A wani labarin kuma El-Rufa’i Ya Bayyana Yadda Alaƙarsa Tayi Tsami da Jonathan a Mulkinsa, Yace Ya Kusa Tura Shi Gidan Gyaran Hali

Gwamnan Kaduna , Nasir Elrufa'i, ya bayyana yadda alaƙarsa ta yi tsami tsakaninsa da tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan.

Yace duk da cewa Jonathan babban amininsa ne tun yana mataimakin gwamnan Bayelsa, amma saida ya matsa masa lamba sabida wasu yan karaɗi sun ziga shi kuma ya ɗauka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel