El-Rufa’i Ya Bayyana Yadda Alaƙarsa Tayi Tsami da Jonathan a Mulkinsa, Yace Ya Kusa Tura Shi Gidan Gyaran Hali
- Gwamnan Kaduna, Nasir Elrufa'i, ya bayyana yadda alaƙarsa ta yi tsami tsakaninsa da tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan
- Yace duk da cewa Jonathan babban amininsa ne tun yana mataimakin gwamnan Bayelsa, amma saida ya matsa masa lamba sabida wasu yan karaɗi sun ziga shi kuma ya ɗauka
- Gwamnan yace an daɗe ana danganta shi da tsayawa takarar shugabancin ƙasar nan tun shekarar 2006, lokacin yana ministan Abuja
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i, yace tsohon shugaban ƙasa, Dr. Goodluck Ebele Jonathan, ya kusan tura shi gidan gyaran hali saboda yana tunanin shi barazana ce ga ƙudirinsa na komawa kan mulki a karo na biyu.
KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Wasu ’Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Shugaban Ƙungiyar Miyetti Allah
Gwamna El-rufa'i a wata tattaunawa da aka buga a 'The point' yace duk da cewa Jonathan babban abokinshi ne tun sanda yake mataimakin gwamna a jihar Bayelsa, amma ya matsa mishi lamba saboda ya amince da waɗanda suka faɗa masa cewa shi barazana ce gareshi.
Gwamnan yace ya fara samun matsin lamba ne daga Jonathan tun a shekarar 2006 lokacin da yake riƙe da babban birnin tarayya, Abuja, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Gwamnan yace:
"Wasu na kusa da Jonathan sun faɗa masa cewa ni barazana ce kuma matuƙar yana son komawa kan madafun iko a karo na biyu, to ya kamata ya fidda ni daga gasar, hakan yasa Jonathan ya cigaba da matsamin lamba kamar yadda Yar'adua ya fara."
"Na kasance ana danganta ni da taka takarar shugabancin ƙasar nan kamar yadda na faɗa tun 2005, 2006 shekaru 15 kenan da suka wuce. Nasha wahala saboda haka, saura kaɗan Jonathan ya tura ni gidan gyaran hali saboda haka."
KARANTA ANAN: Dalilin da Yasa Aka Samu Tsaiko a Dawo da Miliyan £4.2M da Ibori Ya Sace, Malami Yayi Bayani
"Sunana ya daɗe yana yawo dangane da tsayawa takarar shugaban ƙasa tun 2006, tun lokacin ina ministan Abuja. Mutane suka fara yaɗa cewa Obasanjo na ƙoƙarin miƙa mulki gareni."
"Na kusa da marigayi Yar'adua sun faɗa masa, Obasanjo ya ware sunan mutane biyu da zai zaɓi ɗaya ya gaje shi, kuma sunan Yar'adua ne da nawa, wanda ƙaryace kawai tun a wancan lokacin." inji shi.
Gwamnan ya cigaba da cewa daga wannan lokacin Yar'adua ya fara tunanin ni barazana ne ga kudirinsa na takarar shugaban ƙasa.
Dangane da matsalar tsaro kuwa, gwamnan yace gwamnatinsa na aiki tuƙuru, kuma tana amfani da duk wata kafa data samu domin ganin an warware matsalar.
A wani labarin kuma Yan Najeriya Zasu Sami Kwanciyar Hankali a Mulkin Buhari, Bola Tinubu
Jagoran jam'iyya mai mulki APC, Bola Tinubu, ya bayyana ƙwarin guiwarsa cewa yan Najeriya zasu samu kwanciyar hankali a ƙarƙashin mulkin Buhari.
Bola Tinubu yace shugaban ƙasa Buhari ba zaiso a cigaba da kashe al'ummarsa ba kuma ba zaiso ana sace su ba.
Asali: Legit.ng