Ya Kamata CBN Ya Biya 100 Miliyan Na Fansar Ɗaliban Greenfield Tun Kafin Lokaci Ya Ƙure, Sheikh Gumi

Ya Kamata CBN Ya Biya 100 Miliyan Na Fansar Ɗaliban Greenfield Tun Kafin Lokaci Ya Ƙure, Sheikh Gumi

- Sheikh Gumi yayi kira ga gwamnati da kada ta ɗauki lamarin barazanar yan bindigan da suka yi garkuwa da ɗaliban jami'ar Greenfield da sauki

- A cewar shehin Malamin, kuɗin da suka nema suna da matuƙar yawa kuma gwamnati zata iya amfani da kuɗin a kama su

- A zantawar da akayi da ɗaya daga cikin yan bindigan ya bayyana cewa sai an biya su 100 miliyan da kuma mashin ɗin hawa 10 kafin su saki ɗaliban

Shahararren malamin addinin musuluncin nan, Sheikh Ahmad Gumi, a ranar Talata ya roƙi gwamnati kada ta ɗauki barazanar da yan bindigan da suka sace ɗaliban jami'ar Greenfield Kaduna da wasa.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Wasu ’Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Shugaban Ƙungiyar Miyetti Allah

Gumi ya bayyana haka ne a wata zantawa da yayi da Punch, yace babban bankin Najeriya CBN, shine ya kamata ya biya 100 miliyan da yan bindigan suka nema.

Yayi wannan kiran ne yayin da daya daga cikin iyayen ɗaliban ya koka da cewa har yanzun yan bindigan na nan a matsayar su ta sai an biya 100 miliyan.

Ya Kamata CBN Ya Biya 100 Miliyan Na Fansar Ɗaliban Greenfield Tun Kafin Lokaci Ya Ƙure, Sheikh Gumi
Ya Kamata CBN Ya Biya 100 Miliyan Na Fansar Ɗaliban Greenfield Tun Kafin Lokaci Ya Ƙure, Sheikh Gumi Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Mutumin wanda ya zanta da ɗaya daga cikin wakilan Punch a Kaduna ya nemi a sakaya sunanshi, yace har yanzun yan bindigan na nan a kan bakarsu ko a biya ko kuma su hallaka ɗaliban.

Dr. Gumi yace:

"Kuɗin da suka bukata sun yi yawa, idan na baka tsabar waɗannan kuɗin ba zaka iya gudu da su ba, ba wanda zai iya gudu dasu."

"To me zai hana mu basu kuɗin su saki yaran daga nan sai mu kamo su mu dawo da kuɗaɗenmu, daga nan sai muyi abinda yakamata akansu."

"Dabara ce mai sauki, CBN ya bada kuɗinnan, taya zasu ɗauki kuɗin su tafi? Ya kamata muyi tunani."

KARANTA ANAN: Dalilin da Yasa Aka Samu Tsaiko a Dawo da Miliyan £4.2M da Ibori Ya Sace, Malami Yayi Bayani

Aƙalla ɗalibai 23 daga ciki harda wani ma'aikacin jami'ar ɗaya yan bindiga suka yi awon gaba dasu a ranar 20 ga watan Afrilu, 2021.

Amma kwanaki kaɗan bayan haka, yan bindigan suka kashe biyar daga cikinsu kuma suka turo gawarwakinsu.

A ranar Litinin, ɗaya daga cikin yan bindigan, Sani Jalingo, a wata tattaunawa da yayi da ɓangaren hausa na gidan radiyon VOA, Ya buƙaci a biyasu 100 miliyan tare da mashinan hawa 10 kafin su sake su.

Ya kuma yi barazanar cewa, matuƙar gwamnatin jihar Kaduna ko iyayen ɗaliban suka gaza biya musu buƙatar su to zasu kashe ɗaliban.

A wani labarin kuma Gwamnatin Kogi Tayi Cikakken Bayani Kan Kisan da Yan Bindiga Suka Yiwa Kwamishinanta

Gwamnatin jihar Kogi tayi jawabi a kan harin da aka kaima kwamishinan ta da kuma wani shugaban ƙaramar hukuma.

Gwamnatin ta tabbatar da kai harin, inda ta bayyana cewa kwamishinan hukumar fansho ya rasa ransa a harin, kuma an yi awon gaba da shugaban ƙaramar hukumar Yagba ta yamma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262