Bidiyon fasto tana yi wa 'yan cocinta tofin Allah tsine a kan sun ki tara mata kudin bikin bazday

Bidiyon fasto tana yi wa 'yan cocinta tofin Allah tsine a kan sun ki tara mata kudin bikin bazday

- Wata fasto mace ta zage mambobin cocinta da tsinuwa bayan sun ki tara mata kudin shagalin bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta

- Faston da ta bayyana wani bidiyon da ke yawo a kafar sada zumunta, an ji tana kiran mambobin cocinta da shaidanu saboda makon da suka nuna mata

- An ji tana cewa ba amfanin kanta za ta yi da kudin ba, su za ta hadawa abincin da zasu ci saboda wasu daga cikinsu kamar aladu suke

Wata fasto ta yi tofin Allah tsine ga mambobin cocinta sakamakon kin tara mata kudin shagalin murnar bikin zagayowar ranar haihuwarta da suka yi.

A wani bidiyo da ya dinga yawo a kafafen sada zumuntar zamani, an ji faston tana kiran mambobin cocinta da shaidanu saboda kin yi mata wannan kara da suka yi.

"Ko a ranar zagayowar haihuwata, wasu daga cikinku sun ki bada kudi. Ubangiji zai ladabtar da ku saboda baku da tausayi, sai dai kuma idan baku da kudin."

KU KARANTA: Mbaka ya bukaci kwangila bayan goyon bayan Buhari amma aka hana shi, Garba Shehu

Bidiyon fasto tana yi wa 'yan cocinta tofin Allah tsine a kan sun ki tara mata kudin bikin bazday
Bidiyon fasto tana yi wa 'yan cocinta tofin Allah tsine a kan sun ki tara mata kudin bikin bazday. Hoto daga lailanews.com
Asali: UGC

"Ba wai kamar kudin nawa bane, na abincin da zaku zo ku ci ne. Wasu daga cikinku mugun ci garesu kamar aladu kuma sai kun kwasa wani abincin kun tafi da shi gida," faston tace.

Ga bidiyon nan mai karatu ya kalla a kasa:

KU KARANTA: Mbaka ya bukaci kwangila bayan goyon bayan Buhari amma aka hana shi, Garba Shehu

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya, ta musanta rade-radin da ake yi na cewa mayakan Boko Haram sun kai farmaki babban birnin kasar Najeriya.

Ana ta yadawa cewa Boko Haram sun kai hari Abuja bayan samun su da aka yi a jihar Neja dake makwabtaka da su, The Cable ta ruwaito.

Yusuf Mariam, mai magana da yawun rundunar 'yan sandan, ta ce an ga jama'a masu yawa a babura a wasu sassan babban birnin tarayyan, lamarin da ya kawo wannan rade-radin kuma yasa jami'ansu suna fita sintiri.

A wata takarda da ta fitar a ranar Lahadi, Mariam tace an fara tsananta sintiri kuma hakan yana daga cikin matsayar da aka cimmawa bayan taron hadin guiwa na jami'an tsaro da aka yi a ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Online view pixel