Juyin mulki: Hedkwatar tsaro ta ja kunnen sojoji da 'yan siyasa da kakkausar murya

Juyin mulki: Hedkwatar tsaro ta ja kunnen sojoji da 'yan siyasa da kakkausar murya

- Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da biyayyarta ga mulkin shugaban kasa Buhari da kundin tsarin mulkin kasar nan

- Hedkwatar tsaron kasar nan ta ja kunnen manyan sojojinta da 'yan siyasa a kan yunkurin juyin mulki

- Ta ce hankalinta ya kai ga ikirarin Robert Clark wanda ya bukaci a mika mulkin kasar nan ga soji domin sauya tsarinta

Hedkwatar tsaron Najeriya ta ja kunnen 'yan siyasa da manyan dakarun sojin kasar nan a kan shirya juyin mulki.

A wata takarda da hedkwatar tsaron ta fitar a ranar Litinin ta hannun Onyema Nwachukwu, mai magana da yawunta, yace hankalinsu ya kai kan wani tsokacin da Robert Clarke, babban lauya yayi na cewa a mika mulkin kasa ga soji.

Rundunar sojin ta tsame kanta daga wannan tsokacin kuma ta kwatanta shi da mai zagon kasa da damokaradiyya tare da cewa tana biyayya ga mulkin kasar nan, The Cable ta ruwaito.

"Hankalin rundunar soji ya kai ga wani tsokaci da Robert Clark SAN yayi, inda yace a mika mulkin kasar nan ga sojoji saboda a samu sabon tsari," takardar tace.

KU KARANTA: 'Yan sanda sun kama harsasai 753 masu matukar hatsari a Abakaliki, za a kai Abia

Hedkwatar tsaro ta ja kunnen sojojin kasar nan a kan juyin mulki ga gwamnatin Buhari
Hedkwatar tsaro ta ja kunnen sojojin kasar nan a kan juyin mulki ga gwamnatin Buhari. Hoto daga Femi Adesina
Asali: Facebook

KU KARANTA: Shigar Boko Haram Abuja: 'Yan sandan FCT sun magantu, an fara sintiri babu kakkautawa

"Rundunar sojin Najeriya ta tsame kanta daga irin wannan kalami na sukar damokaradiyya. Tana sanar da cewa dakarun sojin kasar nan masu biyayya ne ga gwamnati kuma masu goyon bayan damokaradiyya.

"Za mu cigaba da zama na siyasa, masu goyon bayan gwamnati, masu biyayya ga shugaban kasa, kwamandan dukkan dakarun sojin kasa nan, Shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma gyararren kundun tsarin mulkin kasa na 1999.

"Za mu cigaba da sauke nauyinmu kamar yadda kundun tsarin mulkin ya nuna cike da kwarewa, ballantana wurin kare damokaradiyyya, tsaron kasa tare da baiwa rayuka da kadarori tsaro."

Hedkwatar tsaron ta ja kunnen 'yan siyasa da sojojin kasar nan da kada su fara duba ko tunanin yin juyin mulki domin zasu fuskanci fushin hukuma idan aka kama su.

A wani labari na daban, an samu hargitsi da tashin hankali a yankin Gangare na fitacciyar kasuwar Mile 12 dake karamar hukumar Kosefe na jihar Legas a ranar Juma'a bayan an zargi wani kwamandan 'yan sintiri mai suna Haladu Muhammed da yi wa Annabi batanci.

Daily Trust ta tattaro yadda wasu fusatattun matasa suka zargesa da yin kalaman batanci ga Annabi Muhammad, lamarin da yasa suka kai masa farmaki.

Kafin jami'an tsaro su kaiwa wanda ake zargin dauki, an kone motarsa kuma an farfashe gidansa. Wani ganau ba jiyau ba mai suna Usman Adam Sarauta, ya tabbatar da cewa matasan sun hada da jami'an tsaron da suka gaggauta zuwa wurin bayan kiransu da aka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags:
NDA