Karin Bayani: Boko Haram Sun Dira Bauchi, Sun Mamaye Kananan Hukumomi Hudu

Karin Bayani: Boko Haram Sun Dira Bauchi, Sun Mamaye Kananan Hukumomi Hudu

- Maharan Boko Haram sun shiga wasu sassan jihar Bauchi, sun mamaye kananan hukumomi hudu

- Gwamnatin jihar Bauchi ta tabbatar da faruwar lamarin, ta kuma yi kokarin dasa jami'an tsaro a inda ya dace

- Hakazalika jami'an tsaro sun kame wasu da ake zargin sun lalata gidan talabijin na Gamawa a jihar ta Bauchi

Maharan Boko Haram daga jihar Yobe mai makwabtaka da jihar Bauchi sun kutsa cikin kananan hukumomi hudu na jihar Bauchi, inda suka lalata wasu wurare.

Sakataren gwamnatin jihar Bauchi (SSG), Alhaji Sabiu Baba, ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a ranar Litinin.

Ya lissafa Zaki, Gamawa, Darazo da Dambam daga cikin kananan hukumomin da abin ya shafa.

Rahotannin sun nuna cewa maharan sun lalata mashinan sadarwa a Gamawa, Daily Trust ta rahoto.

KU KARANTA: Mai Sana'ar Yankan Farcen da ke Samun Sama da N45,000 a Wata

Da dumidumi: Boko Haram sun dira Bauchi, sun mamaye wani yanki
Da dumidumi: Boko Haram sun dira Bauchi, sun mamaye wani yanki Hoto: saharareporters.com

Baba ya ce jami'an tsaro sun kama mutane biyar da ake zargi da lalata gidan talabijin na Gamawa, ya kara da cewa tuni gwamnatin jihar ta karfafa tsaro a yankunan da ke makwabtaka da ita.

Ya ce gwamnatin jihar ta gano wasu barazanar tsaro da ke da nasaba da kwararar mutane zuwa cikin jihar daga Yobe inda kungiyar Boko Haram ke yin barna.

Baba ya ce Gwamna Bala Mohammed ya samar da goyon bayan da ake bukata ga jami'an tsaro don karfafa sintiri da sanya ido, musamman al'ummomin kan iyaka da Yobe.

Dangane da batun 'yan gudun hijira, Baba ya ba da tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta hada hannu da al'ummomin da abin ya shafa domin gano wadanda suka rasa muhallansu domin ba su tallafi na gaggawa don rage musu radadin wahalar da suke ciki.

A nasa jawabin a yayin gabatar da jawabin, kwamishinan 'yan sanda na jihar Bauchi, Sylvester Abiodun Alabi, ya ba da tabbacin cewa 'yan sanda za su hada gwiwa da jami'an tsaro don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama'a.

Ya kuma yi kira ga mazauna yankin da su bai wa jami'an tsaro bayanai da suka dace na ayyukan masu aikata laifi kuma su guji rufa wa bata-gari asiri.

KU KARANTA: Na Fara Addu’a Allah Ya Tsige Shugaba Buhari Daga Mulki, in ji Fasto Wale Oke

A wani labarin, Akalla mutum daya farar hula ya rasa ransa yayin da wasu biyar suka jikkata lokacin da wasu da ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne suka yi yunkurin kutsawa cikin garin Rann, hedkwatar karamar hukumar Kala-Balge da ke jihar Borno, in ji majiyar tsaro.

Lamarin ya faru ne lokacin da haramtacciyar kungiyar ta mamaye garin Rann da misalin karfe 6:15 na maraice suna harbe-harbe amma suka gamu da turjiya daga sojojin Najeriya.

Wata majiyar tsaro ta tabbatar da cewa sojoji sun yi amfani da bindigoginsu a yayin harin da aka kai lamarin da ya haifar da sakamakon lalata motar bindigogi ta maharan, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel