Ku Kawar da Mulkin APC Idan Baku Gamsu Ba Da Shi Ba, Gwamnan APC Ya Baiwa Matasa Shawara

Ku Kawar da Mulkin APC Idan Baku Gamsu Ba Da Shi Ba, Gwamnan APC Ya Baiwa Matasa Shawara

- Shekaru kaɗan suka rage babban zaɓen 2023 ya iso amma gwamna Fayemi ya shawarci matasa su fara aiki tun kafin zuwan zaɓen

- Gwamnan Ekiti yace maimakon damuwa da yawan ƙorafi, duk wadanda basa goyon bayan mulkin APC zasu iya haɗa kansu su kawar da ita a zaɓe mai zuwa.

- Jigon jam'iyyar APC ɗin ya kuma yi magana a kan ƙalubalen tsaro da ƙasar nan ke fama dashi, yace akwai buƙatar a zauna a sake gyara tsarin tsaro gaba ɗaya

Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, yace Duk wanda baya jin dadin salon wannan mulkin ƙarƙashin jagorancin jam'iyyar APC, yana da damar da zai canza a babban zabe mai zuwa.

KARANTA ANAN: Wasu mazauna Geidam sun bayyana yadda yan Boko Haram ke musu wa'azi bayan sun ƙwace iko

Gwamnan ya baiwa matasan ƙasar nan shawara, yace zasu iya haɗa kansu su yaƙi jam'iyya mai mulki matuƙar basu gamsu da salon mulkinta ba.

Fayemi yace maimakon ƙorafin da suke yi sabida yanayin da ƙasar ke ciki, kamata yayi matasan su fara ƙoƙari tun yanzu suyi amfani da damarsu da demokaraɗiyya ta basu, su canza APC idan hakan suke buƙata.

Ku fitar da APC daga Mulki idan baku gamsu ba, Gwamnan APC ya baiwa Matasa shawara
Ku fitar da APC daga Mulki idan baku gamsu ba, Gwamnan APC ya baiwa Matasa shawara Hoto: legit.ng
Asali: UGC

Gwamnan wanda jagora ne a jam'iyyar APC, yayi wannan jawabi ne a ranar 1 ga watan Mayu, yayin da yake jawabi a wani shiri da cibiyar kiristoci ke shiryawa duk shekara mai suna 'The Platform' a Iganmu, jihar Lagos.

Gwamnan yace:

"Wani zaɓen zai zo nan gaba, idan baku gamsu da abinda APC keyi ba, ku haɗa kanku, ku daina yawan ƙorafe-ƙorafe, ku shirya yaƙar jam'iyyar, ku nemi haɗin kan mutane waɗanda suma suke shirya hakan, ku fitar da jam'iyyar APC daga mulki."

KARANTA ANAN: Dalilin da Yasa Zamu Cire Tallafin Man Fetur, Gwamnatin Tarayya Tayi Bayani

"Kuna da cikakkiyar damar yin haka, ku zaɓi waɗanda kuke ganin zasu yi abinda ya dace, bawai kuzo kuna ƙirƙirar wani abu mara tsari ba."

A wani rahoton da Legit.ng ta tattaro, gwamnan yace akwai buƙatar a canza gaba ɗaya tsarin da ake amfani dashi wajen yaƙar yan ta'adda.

Fayemi ya bayyana cewa tsarin tsaron ƙasar nan da ake tafiya akansa a yanzun, bazai haifar da ɗa mai ido ba.

"A wannan lokacin ku yi kira a gyara gaba ɗaya tsarin tsaron ƙasar nan." Gwamnan ya baiwa matasa shawara.

A wani labarin kuma APC Ta Maida Zazzafan Martani Ga Gwamnonin PDP a kan matsalar tsaro

Jam'iyyar APC ta maida zazzafan martani a kan wasu jawabai da gwamnonin PDP suka yi wajen nuna damuwarsu da yawaitar hare-haren yan ta'adda a sassan ƙasar nan.

APC tayi wannan martani ne a wani jawabi data fitar a shafinta na Tuwita ɗauke da saka hannun sakataren jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel