Wasu mazauna Geidam sun bayyana yadda yan Boko Haram ke musu wa'azi bayan sun ƙwace iko

Wasu mazauna Geidam sun bayyana yadda yan Boko Haram ke musu wa'azi bayan sun ƙwace iko

- Mazauna garin Geidam da yan Boko Haram suka kwace iko dashi sun bayyana irin halin ƙuncin da suka shiga saboda harin mayaƙan Boko Haram.

- Rahotanni sun bayyana cewa yan ta'addan na gudanar da wa'azin su, suna kira ga mutanen da suka rage a garin da su karɓi da'awarsu ta tsattsauran ra'ayin Jihadi

- Wata Majiya ta ƙara da cewa Yan Boko Haram ɗin sun ƙwace iko da gonaki har sun fara shirin yin noma a garin

Mambobin ƙungiyar Boko Haram sun ƙwace iko da gonaki da kuma ayyukan gona a garin Geidam, jihar Yobe kamar yadda Punch ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa yan ta'addan, waɗanda suka kori mafi yawancin mutanen garin, sun fara yiwa mutanen da suka rage wa'azi akan jihadi, sannan kuma suna basu kyautar kuɗi.

KARANTA ANAN: Gwamnatin Bauchi ta dakatar da wani malamin addinin musulunci Daga gudanar da Wa'azi

Gambo Abdullahi, wani ɗan asalin garin Geidam dake zama a Damaturu, yace har yanzun garin na hannun yan ta'adda yayin da sojojin Najeriya na can yammacin garin.

Wasu mazauna Geidam sun bayyana yadda yan Boko Haram ke musu wa'azi bayan sun ƙwace iko
Wasu mazauna Geidam sun bayyana yadda yan Boko Haram ke musu wa'azi bayan sun ƙwace iko Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Yace: "Har yanzun yan Boko Haram na cikin Geidam, kuma su keda ikon gudanarwa a garin. Tunda suka kori mutanen garin, sun cigaba da yin wa'azi kan tsattsauran ra'ayin jihadi ga mutanen da suka rage."

"Bayan sun kammala wa'azin su, suna bayar da kuɗi N20,000 domin su jawo hankalin mutanen su shigo ƙungiyarsu."

"Hakanan kuma yan ta'addan sun kwace iko da gonakin mutane, Kuma sun fara gyaran gonakin ta hanyar cire ciyawa da sauransu, kai kace zasu daɗe ne a garin."

ƘARANTA ANAN: Sakataren Amurka yayi magana kan matsalar tsaro bayan ganawarsa da Shugaba Buhari

A wata majiyar daga Damaturu babban birnin jihar, Muhammed Sale, yace wasu daga cikin mutanen da suka rage a garin sun fara guduwa zuwa ƙauyen Kalgeri ɗake kusa da Geidam ɗin.

Yace: "Ba'a hada-hadar abin hawa zuwa garin Geidam, duk wani abun hawa a Kalgeri yake tsayawa, iyayena sun baro Geidam zuwa Damaturu, saida suka yi tafiyar kafa mai tsawo zuwa Kalgeri sannan suka sami mota zuwa Damaturu."

A wani labarin kuma Gwamnatin Kaduna ta bayyana dalilin da yasa yan bindiga suka dirar ma Jihar da ta'addanci

Gwamnatin jihar Kaduna ta yi Allah wadai da kisan da yan bindiga keyiwa ɗalibai masu karatu a makarantun gaba da sakandire na Jihar.

Gwamnatin tace yan bindigar na haka ne don kawai su jawo hankalinta ta canza matsayarta na 'Ba biyan kuɗin fansa' da kuma 'Ba maganar sulhu da yan bindiga'

Asali: Legit.ng

Online view pixel