Rashin Tsaro: APC Ta Maida Zazzafan Martani Ga Gwamnonin PDP

Rashin Tsaro: APC Ta Maida Zazzafan Martani Ga Gwamnonin PDP

- Jam'iyyar APC ta maida zazzafan martani a kan wasu jawabai da gwamnonin PDP suka yi wajen nuna damuwarsu da yawaitar hare-haren yan ta'adda a sassan ƙasar nan

- APC tayi wannan martani ne a wani jawabi data fitar a shafinta na Tuwita ɗauke da saka hannun sakataren jam'iyyar

- Ta kuma roƙi gwamnonin da masu ruwa da tsaki a ɓangaren tsaro da su cigaba da baiwa shugaba Buhari goyon baya

Jam'iyyar APC tayi martani game da wasu jawabai da gwamnonin PDP suka yi kan yawaitar kai hare-hare a wasu sassan ƙasar nan.

KARANTA ANAN: Wasu mazauna Geidam sun bayyana yadda yan Boko Haram ke musu wa'azi bayan sun ƙwace iko

A kwanakin baya shuwagabannin PDP sun nuna matuƙar damuwa kan matsalar tsaron ƙasar nan dake kara ninkuwa kullum kwana.

A wani jawabi da APC ta fitar a shafinta na dandalin sada zumunta Tuwita ɗauke da saka hannun Sakataren kwamitin riƙo, Sen. John James Akpanudoedehe, jam'iyyar ta nuna rashin jin daɗinta kan cigaba da ƙaruwar matsalar.

Rashin Tsaro: APC Ta Maida Zazzafan Martani Ga Gwamnonin PDP
Rashin Tsaro: APC Ta Maida Zazzafan Martani Ga Gwamnonin PDP Hoto: @OfficialAPCng
Asali: Twitter

APC ta ƙara da cewa ya kamata mutane su daina shakka kuma shugaba Buhari na da ƙarfin guiwar magance dukkan waɗannan matsalolin da Najeriya ke fuskanta.

Tace cikakkun yan Najeriya kuma masu kishi su guji saka siyasa a cikin lamarin, da kuma duk wani abu da zai kawo rarrabuwar kai.

A jawabin data fitar, APC tace:

"Muna kira ga masu ruwa da tsaki, da kuma yan Najeriya masu kishi da kada su saka siyasa a fannin tsaron ƙasar nan. A wannan lokacin, aikin mu a matsayin mu na yan ƙasa nagari yafi mana muhimmanci fiye da siyasar mu."

KARANTA ANAN: Kashi 70% na matasan Najeriya yan zaman kashe wando ne, Inji NOA

"Ya kamata gwamnonin PDP su sani cewa rarrabuwar kai ba zai haifar da ɗa mai ido ba, sai dai ya ƙarawa yan ta'addan ƙwarin guiwa."

"Yanzu haka, ƙwararrun masu bincike na cigaba da aikinsu domin zaƙulo da gano mutanen dake ɗaukar nauyin Yan ta'adda, Shugaba Buhari ya bada umarnin yin duk abinda ya dace a binciken."

"Muna da ƙarfin guiwar cewa, gwamnonin PDP da sauran masu ruwa da tsaki zasu cigaba da baiwa gwamnati goyon baya a ƙoƙarin da take yi na ganin zaman lafiya ya dawo a faɗin ƙasar nan." inji APC.

A wani labarin kuma Gwamnan Rivers Ya Caccaki APC, Yace Babu Wani Mai Hankali da Zai So APC a 2023

Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike , ya caccaki jam'iyya mai mulki da ƙoƙarinta na daƙile shirin gyaran dokokin zaɓe.

Gwamnan yace APC na jin tsoron ayi gyaran ne saboda yan Najeriya sun dawo daga rakiyarta kuma ba zasu zaɓi jam'iyyar ba a zaɓe mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel