'Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari, Sun sace Mahaifiyar Dan Majalisan Tare da Kashe Mutane 2 a Neja

'Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari, Sun sace Mahaifiyar Dan Majalisan Tare da Kashe Mutane 2 a Neja

- ‘Yan bindiga sun kai hari jihar Neja a daren ranar Alhamis inda suka yi awon gaba da wasu mutane, ciki har da mahaifiyar wani dan majalisa, Honarabul Bello

- Rahoton ya nuna cewa tuni masu garkuwan suka tuntubi dan majalisar inda suke neman kudin fansa na N100m

- Satar matar mai shekaru 78 na zuwa ne a ranar da aka kashe mutane biyu sannan aka sace wasu daga karamar hukumar Rafi

Wasu rahotanni sun ce wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun sace Hajiya Salamatu Ahmadu, mahaifiyar dan majalisar dokokin jihar Neja, Alhaji Bello Ahmed Agwara mai shekaru 78.

Jaridar ThisDay ta rahoto cewa an sace tsohuwar ne da misalin karfe 9:00 na daren ranar Alhamis, 29 ga Afrilu.

KU KARANTA KUMA: Father Mbaka da Buhari: ’Yan Najeriya Sun Goyi Bayan Fitaccen Faston, Sun Caccaki Fadar Shugaban Kasa

'Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari, Sun sace Mahaifiyar Dan Majalisan Tare da Kashe Mutane 2 a Neja
'Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari, Sun sace Mahaifiyar Dan Majalisan Tare da Kashe Mutane 2 a Neja Hoto: @NigerStateNG
Asali: Twitter

A cewar rahoton, wasu 'yan bindiga dauke da muggan makamai wadanda suka zo kan babura hudu sun afkawa gidan dan majalisar dokokin jihar Neja da ke garin Agwara.

Ganau sun bayyana cewa masu laifin sun fara yin harbi ba kakkautawa yayin da mutane suka tsere don tsiratar da ransu.

An tattaro cewa yan bindigan sun nufi gidan dan majalisar inda suka yi awon gaba da mahaifiyarsa da kuma wasu mazauna garin zuwa wani wurin da ba a sani ba.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da aka kashe mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu da dama a Tegina da ke karamar hukumar Rafi ita ma a wannan ranar.

Lokacin da jaridar ThisDay ta tuntube shi, wani babban jami’in majalisar dokokin jihar wanda ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da sace mahaifiyar dan majalisar.

Jami'in ya ce:

"Mun je gidansa a Minna don yi masa jaje."

Rahoton ya nuna cewa tuni yan fashin suka yi magana da dan majalisar kuma suna neman a biya su N100m kafin matar ta samu yancinta.

KU KARANTA KUMA: 'Yan Bindiga' Ya'yan Mu Ne, Na Kan Ji Bakin Ciki Idan Aka Kashesu, Gwamna Umahi Yana Neman Sulhu

Duk kokarin da aka yi don tuntubar Agwara ya ci tura saboda bai daga kiran wayarsa ko amsa sakonnin tes.

A gefe guda, Shugaban kungiyar gwamnonin Nigeria kuma gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi ya ce ta'addanci ya yi sauki a Nigeria tun lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi ragamar mulki a 2015, The Punch ta ruwaito.

Tsohon ministan ya ce kowa na rayuwa cikin tsoro duk da cewa jam'iyyar da ke mulki a kasar ta samu nasarori kan yaki da ta'addanci amma akwai bukatar ta kara jajircewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng