Dakarun Rundunar Sojojin Chadi Sun Kashe Ƴan Tawaye da Dama a Wani Arangama da Suka Yi

Dakarun Rundunar Sojojin Chadi Sun Kashe Ƴan Tawaye da Dama a Wani Arangama da Suka Yi

- Sojojin Chadi sun halaka daruruwan yan tawaye a wani fafatawa da suka yi

- Sai dai rundunar ta ce ta rasa dakarunta guda shida a arangamar

- Sojojin Chadi na fuskantar ƙarin ƙalubalen daga yan adawasaboda kwace mulki da suka yi bayan mutuwar Idriss Deby

Rahotanni sun kawo cewa daruruwan mayakan yan tawayen kasar Chadi sun rasa rayukansu a wani arangama da suka yi da rundunar sojojin kasar na tsawon kwanaki biyu a yankin yammacin kasar.

An tattaro cewa kakakin rundunar sojojin ya ce, su ma sun rasa dakaru shida a fafatawan.

KU KARANTA KUMA: 'Yan Bindiga' Ya'yan Mu Ne, Na Kan Ji Bakin Ciki Idan Aka Kashe su, Gwamna Umahi Yana Neman Tattaunawa

Dakarun Rundunar Sojojin Chadi Sun Kashe Ƴan Tawaye da Dama a Wani Arangama da Suka Yi
Dakarun Rundunar Sojojin Chadi Sun Kashe Ƴan Tawaye da Dama a Wani Arangama da Suka Yi Hoto: BBC
Asali: UGC

Ana dai ta fafata yaƙi a yankin da ke da nisan kilomita 250 daga babban birnin kasar, kusa da inda aka yi wa Shugaba Idriss Deby mummunan raunin da ya yi sanadin rasuwarsa a watan da ya gabata, sashin Hausa na BBC ta ruwaito.

Sojojin na kokarin hana ‘yan tawayen da ake kira FACT shiga N’djamena, babban birnin kasar.

Sojojin Chadi suna samun goyon bayan dakarun Faransa amma suna yaki ne da yan tawayen da suka samu makamai daga yaƙin Libya.

Sojojin Chadi kuma suna fuskantar wani ƙarin ƙalubalen daga yan adawa, musamman masu zanga-zangar adawa da kwace mulki da sojoji suka yi bayan mutuwar Idriss Deby.

KU KARANTA KUMA: Zan Yi Duk Me Yiwuwa Don Dawo da Zaman Lafiya da Tsaro a Najeriya – Buhari

A wani labarin, mun ji a baya cewa fadan da aka gwabza tsakanin sojoji da masu da'awar jihadi a yankin tafkin Chadi a ranar Talata ya yi sanadiyyar rayukan 'yan kasar ta Chadi akalla 12, kamar yadda wani gwamnan lardin ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na AFP.

Mahamat Fadoul Mackaye ya ce an kuma kashe mayakan 40 bayan harin da aka kai kan wani sansanin sojoji a yankin na fadama da kungiyoyin jihadi da suka hada da Boko Haram da ke Najeriya da kuma wani reshe na kungiyar ISWAP suka yi a baya-bayan nan.

"Dakarun tsaron sun mai da martani mai karfin gaske don fatattakar abokan gaba, wadanda suka bar gawarwaki 40 da makamai, amma muna bakin cikin rashin sojoji 12," in ji Mackaye ga AFP ta wayar tarho.

Asali: Legit.ng

Online view pixel