Dangote da Alakija sun shiga jerin ƴan Nigeria da suka fi kyauta a 2021

Dangote da Alakija sun shiga jerin ƴan Nigeria da suka fi kyauta a 2021

Attajirai da dama suna amfani da dukiyoyinsu domin tallafawa masu karamin karfi ba tare da an roke su ba, mafi yawancinsu suna kafa gidauniya da sunansu ko na kamfanoninsu ko kuma wasu lokutan a boye suke taimakon.

Legit.ng ya haska fitilarsa kan wasu attajiran yan Nigeria da yan kasuwa da ke amfani da dukiyoyinsu domin farantawa jama'a rai ta hanyar basu tallafi.

DUBA WANNAN: Buhari Ya Amince a Fara Aiwatar Da Shirin Rage Talauci Na Ƙasa a Nigeria

Dangote da Alakija sun shiga jerin ƴan Nigeria da suka fi kyauta a 2021
Dangote da Alakija sun shiga jerin ƴan Nigeria da suka fi kyauta a 2021. Photo Credit: Pius Utomi Ekpei, Wei Leng Tay, George Osodi
Asali: Getty Images

1. Aliko Dangote

Dan kasuwa Aliko Dangote shine na farko a jerin yan Nigeria da suka fi yin kyauta da dukiyarsu.

Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka ya mallaki kimanin Dala biliyan 11.6 a cewar Forbes, yana da hanyoyi daban-daban da ya ke fitar da kudi don tallafawa jama'a.

Dangote, ta hanyar amfani da gidauniyarsa na Aliko Dangote Foundation, ADF, da aka yi wa rajista a 1994 ya kashe fiye da Dallar Amurka miliyan 100 wurin ayyukan taimakawa jama'a a cewar Persecondnews.

A baya bayan nan ADF ta kaddamar da wani shirin tallafawa mutane da harin yan bindiga ya shafa a Zamfara inda aka rabar da Naira biliyan 3.924 ga mata da matasa 390492 a jihohin Nigeria a matsayin jari.

2. Tony Elumelu

Shugaban United Bank for Africa, UBA, Tony Elumelu mutum ne da ya yi fice wurin tallafawa jama'a.

Ya taimakawa matasa masu sana'a da yawa ta hanyar amfani da gidauniyarsa na Tony Elemelu Foundation, TEF, da aka kafa a 2010.

A karkashin gidauniyar an ware kimanin Dala miliyan 100 domin binciko da taimakawa matasa 10,000 kawo yanzu. Baya da wannan akwai wasu ayyukan da ya ke yi da dama na taimakon mutane.

KU KARANTA: 'Yan Bindiga Sun Buɗewa Ayarin Motocin Sanata Wuta a Kogi

3. T.Y. Danjuma

Tsohon Janar na Soja mai murabus, tsohon ministan tsaro kuma shugaban kamfanin South Atlantic, T.Y. Danjuma na daya daga cikin mutanen da ke tallafawa mutane sosai a Nigeria.

Dan kasuwar, ta hanyar amfani da gidauniyarsa na TY Danjuma Foundation yana samar wa yara da matasa ilimi, magunguna da wasu ababen rayuwa kyauta.

Gidauniyarsa kuma tana hadin gwiwa da wasu kungiyoyin masu taimakon mutane wurin tallfawa mutanen karkara.

4. Folorunso Alakija

Folorunso Alakija biloniyar yar kasuwa ce mai zuciyar taimakawa mutane.

Gidauniyarta na Rose of Sharon Foundation wanda ke mayar da hankali wurin taimakawa marayu da matan da mazajensu suka rasu ya samar da gidaje 630 ga matan da mazansu suka rasu sannan ya basu tallafi na lafiya da lauyoyi kyauta.

5. Toyin Saraki

Toyin Saraki, matar tsohon shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ta hanyar amfani da gidauniyarta na Wellbeing Foundation Africa (WBFA) ya taimakawa iyalai da dama ta hanyar karfafawa mata gwiwa da basu jari a garuruwa.

A wani rahoton daban, Mallam Garba Shehu ya caccaki wadanda suke sukar Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Dr Isa Pantami saboda rashin yafe masa abin da ya yi a baya, Channels Television ta ruwaito.

Ya na ganin rashin yafewa ministan kan maganganun da ya yi na goyon bayan kungiyoyi masu tsatsauran ra'ayi ya fi muni kan laifin da ministan ya aikata.

Babban mai taimakawa shugaban kasar a bangaren watsa labarai ya yi wannan kalaman ne a lokacin da ya bayyana a shirin Politics Today na Channels Television a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164