2023: Ahmed Musa, Tuface da Omotola sun samu tikitin takara kyauta a ADC

2023: Ahmed Musa, Tuface da Omotola sun samu tikitin takara kyauta a ADC

- Jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) ta yi wa wasu taurari a Nigeria tayin tikitin takara kyauta a 2023

- Taurarin da aka yi wa tayin sun hada da Dan kwallo Ahmed Musa, Mawaki Tuface da Jarumar Nollywood, Omotola

- Jam'iyyar ADC ta ce ta yi wannan tayin ne domin karfafawa matasa da mata gwiwa su shiga siyasa a rika damawa da su

Jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) ta bawa fitaccen mawaki Innocent Idibia da aka fi sani da Tuface, Jarumar Nollywood Omotola Jalade-Ekeinde, shahararren dan kwallo Ahmed Musa da DJ Switch tikitin takarar ko wane kujera da suke so a babban zaben 2023.

The Nation ta ruwaito cewa shugaban jam'iyyar na kasa Ralph Okey Nwosu ne ya sanar da hakan yayin da ya ke karbar satifiket na goyon bayan baya a 'matsayin jam'iyyar ta matasa da matan Nigeria' domin zaben 2023.

2023: Ahmed Musa, Tuface da Omotola sun samu tikitin takara kyauta a ADC
2023: Ahmed Musa, Tuface da Omotola sun samu tikitin takara kyauta a ADC. Hoto: @TheNationNews

DUBA WANNAN: Dangote da Alakija sun shiga jerin ƴan Nigeria da suka fi kyauta a 2021

Nwosu ya ce jam'iyyar ta yanke shawarar tsayar da jaruman ne a 2023 domin karfafawa matasa gwiwa su shiga siyasa inda ya kara da cewa masu nishantarwar sun fi yan siyasar da aka zaba yi wa Nigeria hidima.

Ya bawa taurarin tabbacin cewa suna iya yin takarar gwamna, sanata ko kuma kujera mafi girma a kasar (shugaban kasa) muddin sun cika ka'idojin da kudin tsarin 1999 ta tanada da dokokin hukumar zabe mai zaman kanta na kasa INEC.

KU KARANTA: 'Yan Bindiga Sun Buɗewa Ayarin Motocin Sanata Wuta a Kogi

Jam'iyyar ta kuma yabawa kyaftin din Super Eagles Ahmed Musa saboda dawowa gida ya bugawa tsohwar kungiyarsa ta Kano Pillars wasa duk da cewa ya buga wasanni a Turai da Asiya na tsawon shekaru.

A wani labarin daban, kun ji cewa an naɗa kakakin majalisar wakilan tarayyar Nigeria, Femi Gbajabiamila da Sanatoci uku da ke wakiltar Legas a matsayin mambobin Kwamitin bawa gwamna shawarwari wato GAC.

Jam'iyyar All Progressives Congress, APC, reshen jihar Legas ne ta bada sanarwar a ranar Laraba, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Sanatoci ukun sune maiɗakin jagorar jam'iyyar APC na ƙasa, Oluremi Tinubu, Solomon Adeola da Tokunbo Abiru.

Asali: Legit.ng

Online view pixel