Gwamnan Rivers Ya Caccaki APC, Yace Babu Wani Mai Hankali da Zai So APC a 2023

Gwamnan Rivers Ya Caccaki APC, Yace Babu Wani Mai Hankali da Zai So APC a 2023

- Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya caccaki jam'iyya mai mulki da ƙoƙarinta na daƙile shirin gyaran dokokin zaɓe

- Gwamnan yace APC na jin tsoron ayi gyaran ne saboda yan Najeriya sun dawo daga rakiyarta kuma ba zasu zaɓi jam'iyyar ba a zaɓe mai zuwa

- Wike wanda tsohon ministan ilimi ne yace babu wani ɗan Najeriya kuma mai hankali da zaiso APC ta sake ɗarewa kujerar mulkin ƙasar nan a zaɓen 2023

Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers ya caccaki jam'iyya mai mulki APC saboda jan kafar da take yi wajen gyaran dokokin zaɓe.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Ƙasar Amurka Ta Bayyana Matsayin Najeriya A Wajenta

Gwamnan yace babu wani ɗan Najeriya mai hankali da zaiso jam'iyyar ta sake ɗarewa mulkin ƙasar nan a zaɓen 2023 dake tafe.

Nyesom Wike ya bayyana haka ne a wani sako da ya fitar a shafinsa na kafar sada zumunta tuwita.

Gwamnan Rivers Ya Caccaki APC, Yace Babu Wani Mai Hankali da Zai So APC a 2023
Gwamnan Rivers Ya Caccaki APC, Yace Babu Wani Mai Hankali da Zai So APC a 2023 Hoto: @GovWike
Asali: Twitter

Wike wanda tsohon ministan ilimi ne ya ƙara da cewa yan Najeriya sun dawo daga rakiyar jam'iyyar ta APC, sannan ya zargi jam'iyyar da ƙoƙarin daƙile shirin gyaran dokokin zaɓen.

KARANTA ANAN: Gwamnan Zamfara ya bada umurnin rusa gidajen masu yi wa 'yan bindiga leƙen asiri

A sakon da gwamnan ya fitar ɗin yace:

"Gyara dokokin zaɓen wata babbar nasara ce ga ƙasar nan, domin gudanar da gyaran alama ce dake nuna za'a gudanar da zaɓen gaskiya-da-gaskiya wanda mutane zasu amince da shi."

"Amma abun takaicin shine, muna gani ana jan ƙafa kan lamarin saboda gwamnati bata son ayi gyaran, don su samu damar murɗe zaɓe nan gaba."

"Sun san mutane sun dawo daga rakiyar gwamnatin su, Kuma babu wani ɗan Najeriya mai hankali da zai so su sake dawowa kan karagar mulkin ƙasar nan."

A wani labarin kuma Gwamnatin Kaduna ta bayyana dalilin da yasa yan bindiga suka dirar ma Jihar da ta'addanci

Gwamnatin jihar Kaduna ta yi Allah wadai da kisan da yan bindiga keyiwa ɗalibai masu karatu a makarantun gaba da sakandire na Jihar.

Gwamnatin tace yan bindigar na haka ne don kawai su jawo hankalinta ta canza matsayarta na 'Ba biyan kuɗin fansa' da kuma 'Ba maganar sulhu da yan bindiga'.

Asali: Legit.ng

Online view pixel