Da Ɗumi-Ɗumi: Ƙasar Amurka Ta Bayyana Matsayin Najeriya A Wajenta

Da Ɗumi-Ɗumi: Ƙasar Amurka Ta Bayyana Matsayin Najeriya A Wajenta

- Amurka ta bayyana kyakkyawar alaƙar dake tsakaninta da Najeriya, inda tace Najeriya na daga cikin abokanta masu matuƙar Muhimmanci

- Wannan ya biyo bayan ziyarar da sakataren ƙasar ta Amurka, Antony J. Blinken, ya kawo Najeriya ranar Talata ta hanyar amfani da fasahar zamani

- A yayin ziyarar, Sakataren ya tattauna da shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da kuma Ministan harkokin ƙasashen waje, Geoffrey Onyeama.

A ranar Talata, Sakataren ƙasar Amurka, Antony J. Blinken, ya ziyarci Najeriya ta hanyar amfani da fasahar zamani (Virtually) inda ya gana da shugaba Buhari da kuma ministan kasashen waje, Geoffrey Onyeama.

KARANTA ANAN: Gwamnatin Kaduna ta bayyana dalilin da yasa yan bindiga suka dirar ma Jihar da ta'addanci

Mutanen uku sun tattauna akan abubuwa da dama, waɗanda suka haɗa da; yadda zasu haɗa kai wajen yaƙar ta'addanci da rashin tsaro, gyaran ɓangaren lafiya, bunƙasa tattalin arziƙi da sauransu.

Hakanan kuma shugaba Buhari ya tattauna da sakataren kan yadda za'a bunƙasa kasuwanci tsakanin ƙasar Amurka da Najeriya, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Bayan wannan tattaunawar ne gwamnatin ƙasar Amurka ta fidda bayani kan alaƙar dake tsakanin ƙasashen biyu.

Da Ɗumi-Ɗumi: Ƙasar Amurka Ta Bayyana Matsayin Najeriya A Wajenta
Da Ɗumi-Ɗumi: Ƙasar Amurka Ta Bayyana Matsayin Najeriya A Wajenta Hoto: @NGRpresident
Asali: Twitter

A bayanin data fitar gwamnatin tace:

"Ƙasar data fi kowacce ƙasa yawan jama'a, damokaradiyya, da kuma tattalin arziƙi a nahiyar Africa, Najeriya tana ɗaya daga cikin abokan mu masu muhimmanci a duniya."

KARANTA ANAN: Majalisar Dattijai Sun Yanke Wata Muhimmiyar Shawara Game Da Matsalar Tsaro, Zasu Gana Da Buhari

"Kasancewar shekarar 2020 tazo da ƙalubale da yawa kuma ta aje tarihi, Najeriya ta fusaknci ƙalubale da yawa a yayin da Ƙasar ke bikin cika shekaru 60 da samun yancin kai."

"Najeriya ita ce ƙasar da aka fi samun mutanen dake zuwa ƙasar Amurka daga Nahiyar Africa, inda akwai yan asalin Najeriya 500,000 dake zaune a ƙasar Amurka."

A wani labarin kuma Wani Sanata Daga Jihar Neja Ya bayyana Wani Adadi Mai Yawa Na Ƙauyukan dake Ƙarƙashin Boko Haram

Wani sanata daga jihar Neja, ya bayyana cewa kauyuka da dama sun koma ƙarƙashin ikon yan ta'addan Boko Haram a jihar.

Sanatan dake wakiltar mazaɓar jihar Neja ta gabas, Sanata Mohammed Sani Musa, ya faɗi haka ne yayin da yake gabatar da kudiri a gaban majalisa kan kashe-kashen dake faruwa a Neja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262