Gwamnan Zamfara ya bada umurnin rusa gidajen masu yi wa 'yan bindiga leƙen asiri

Gwamnan Zamfara ya bada umurnin rusa gidajen masu yi wa 'yan bindiga leƙen asiri

- Gwamnan Zamfara ya sha alwashin rusa duk gidan da aka kama masu kaima yan bindiga labaru a ciki ba tare da bata lokaci ba

- Gwamnan ya faɗi haka ne yayin da ya karɓi baƙuncin takwaransa na jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal

- Gwamnan ya kuma baiwa sarakunan gargajiya umarnin su saka ido kan duk wanda za'a baiwa gidan haya a yankunan su

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, yasha alwashin rusa duk wani gidan da ake boye masu safarar makamai da kuma masu kaiwa yan bindiga labaru.

Gwamnan ya bayyana haka ne ranar Talata, lokacin da ya karɓi baƙuncin gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, tare da yan tawagarsa.

Matawalle ya bada umurnin rusa gidajen masu yi wa 'yan bindiga leken asiri
Matawalle ya bada umurnin rusa gidajen masu yi wa 'yan bindiga leken asiri. Hoto: @Matawalle1
Asali: Facebook

KARANTA ANAN: Gwamnatin Kaduna ta bayyana dalilin da yasa yan bindiga suka dirar ma Jihar da ta'addanci

Tambuwal yaje jihar ne domin ya jajantawa gwamnatin jihar da mutane bisa hare-haren da yan bindiga suka kai a wasu sassan jihar kwanan nan.

Matawalle yace ya bada umarnin a ɗauki duk wani matakin da ya dace wanda ya haɗa da rusa gidan ɓoyon masu kaima yan bindiga labaru, masu safarar makamai da kuma masu ɗaukar nauyin yan bindiga nan take.

Yace wannan matakin ya zama wajibi domin a magance yawaitar harin yan bindiga a wasu sassan jihar, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Ya ƙara da cewa masu ɗaukar nauyin yan ta'addan na rayuwa ne a cikin birane tare da mutane kuma suna kaiwa yan bindigan labaru.

KARANTA ANAN: Rigakafin COVID19: Wata ma'aikaciyar Lafiya ta bayyana halin da ta shiga tunda akai mata rigakafin Astrazeneca

Gwamnan yace:

"Ayyukan masu leken asiri na kaima yan bindiga labaru yana jawo matsaloli da yawa a kan yaƙin da muke yi da yan ta'adda, muna kira ga mutane da su goya mana baya domin mu sami nasara a wannan yaƙi."

"Muna roƙon sarakunan gargajiya da su kasance a ankare kuma su kula wajen mutanen da ake baiwa hayar gidaje a yankunan su. Muna umurtar su da suyi gaggawar kai rahoton duk wanda basu yarda dashi ba zuwa hukumomin tsaro."

Gwamnan ya kuma bayyana cewa matuƙar aka ɗauki matakin saka ido ga waɗanda ba'a yarda da su ba da matukar muhimmanci, to hakan zai rage kashe-kashen mutane.

A wani labarin kuma Fadar Shugaban ƙasa ta bayyana abinda Buhari ya tattauna da sakataren Amurka

Shugaba Buhari ya roki ƙasar Amurka da tazo su haɗa ƙarfi da karfe wajen daƙile kalubalen tsaron da Najeriya ke fama dashi.

Shugaban ya roƙi ƙasar da ta duba yuwuwar dawo da hedkwatar taimakawa ƙasashen Africa (AFRICOM) daga ƙasar Germany zuwa nahiyar Africa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262