Gwamnatin Kaduna ta bayyana dalilin da yasa yan bindiga suka dirar ma Jihar da ta'addanci

Gwamnatin Kaduna ta bayyana dalilin da yasa yan bindiga suka dirar ma Jihar da ta'addanci

- Gwamnatin jihar Kaduna ta yi Allah wadai da kisan da yan bindiga keyiwa ɗalibai masu karatu a makarantun gaba da sakandire na Jihar

- Gwamnatin tace yan bindigar na haka ne don kawai su jawo hankalinta ta canza matsayarta na 'Ba biyan kuɗin fansa' da kuma 'Ba maganar sulhu da yan bindiga'

- Kakakin gwamnan jihar, Muyiwa Adeyeke, shine ya bayyana haka a wani saƙo da ya fitar, yace gwamnati nanan kan matsayarta, ba gudu babu ja da baya

Gwamnatin kaduna tayi Allah wadai da kisan wasu ɗalibai dake karatu a manyan makarantun gaba da sakandire da yan bindiga keyi a jihar.

KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: Fadar Shugaban ƙasa ta bayyana abinda Buhari ya tattauna da sakataren Amurka

A wani jawabi da kakakin gwamnan jihar, Muyiwa Adekeye, ya fitar ranar Talata, ya jajantawa iyalan da abun ya shafa, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Adekeye yace: "Wannan kisan matasan da masu garkuwa da mutanen keyi wani ɓangarene na ƙoƙarin su yaudari gwamnati."

"Kuma suna aikata wannan mummunan ta'addancin ne domin su saka gwamnatin Kaduna ta canza matsayar daga 'Ba biyan kudin fansa, ba tattaunawa' zuwa yadda suke so."

Muyiwa Adekeye ya kuma mai da martani kan wani bidiyo dake yawo a kafafen sada zumunta, wanda ke ɗauke da wata tattaunawa da aka yi da gwamna Malam Nasiru Elrufa'i tun shekarar 2014.

Gwamnatin Kaduna ta fito fili ta bayyana dalilin da yasa yan bindiga suka dirar ma Jihar
Gwamnatin Kaduna ta fito fili ta bayyana dalilin da yasa yan bindiga suka dirar ma Jihar Hoto: @muyiwaadekeye
Asali: Twitter

Ya kuma yi watsi da waɗanda ke zargin gwamnan bisa matsayar da ya ɗauka a kan matsalar sace-sacen mutane a jihar.

KARANTA ANAN: Dalilin da Yasa Yan Arewa Zasu Fi Son Bola Tinubu Ya Zama Magajin Buhari

A cikin bidiyon, Anga gwamnan jihar Kaduna na kira ga gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, tayi amfani da duk wata dama, koda tattaunawa ce wajen kuɓutar da yan Matan Chibok da aka sace.

Yayin da yake kare maganar gwamnan, Adekeye yace:

"Tun daga wancan lokacin da lamarin Chibok ya faru zuwa yanzun, ya nuna cewa matakin da yafi dacewa a ɗauka kan irin waɗannan sace-sacen shine ta hanyar amfani da ƙarfi, wanda hukumomin tsaron mu suke yi."

A wani labarin kuma Gwamnatin Kaduna ta faɗi wani abu mai muhimmanci lokacin da taje Ta'aziyyar Ɗaliban Greenfield da aka kashe

Gwamnatin jihar Kaduna ta tura wakilai ƙarkashin jagorancin kwamishinan Ilimin jihar suje su yiwa iyayen ɗaliban jami'ar Greenfield da yan bindiga suka kashe ta'aziyya.

A jawabinsa na wajen ta'aziyyar, kwamishi nan Ilimin, Shehu Muhammed, yace gwamnati na nan akan bakarta na babu tattaunawar sulhu tsakaninta da yan bindiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262