Za Mu Dauki Mataki Kan Duk Wanda Yake Watsa Hotunan Sojoji da Aka Kashe, Gidan Soja
- Rundunar sojin Najeriya ta gargadi masu watsa hotunan sojojin da suka mutu a fagen daga da su kula
- Rundunar ta koka kan yadda wasu 'yan Najeriya ke watsa hotunan cikin rashin kishin kasa da kin doka
- Ta kuma yi alwashin daukar matakin donka kan masu aikata laifin na ba'a ga sojojin da suka mutu
Sojojin Najeriya sun yi Allah wadai da watsa hotuna “ba kakkautawa” na sojojin da aka kashe ko suka ji rauni a bakin aikinsu, TheCable ta ruwaito.
Mohammed Yerima, mai magana da yawun rundunar soji, a wata sanarwa a ranar Talata, ya ce irin wannan watsa hotunan sojoji a kafafen sada zumunta rashin hankali ne da rashin kishin kasa.
Ya yi tuhuma game da yadda wasu 'yan kasa ke “murna” da dora hotunan sojoji wadanda suka mutu yayin bautawa kasa, yana mai bayyana cewa irin wadannan abubuwan na haifar da damuwa ga iyalan sojojin da abin ya shafa.
KU KARANTA: Babu Shugaban da Zai So Kasarsa Ta Lalace, Ku Dai Ku Hada Kai, Tinubu Ga ’Yan Najeriya
Ya kara da cewa daga yanzu haka sojojin za su dauki matakin da ya dace na shari'a a kan mutanen da aka samu da laifin.
"Sojojin Najeriya sun yi Allah wadai a cikin yanayi mafi tsauri lokacin game da watsa hotuna ba kakkautawa a kan shafukan na ma'aikatan da suka yi shahada a dalilin kare kasa da kuma kare ta daga masu adawa da ita," in ji Yerima.
“Wannan aikin ba wai kawai rashin kishin kasa bane, yana nuni da matukar rashin hankali kuma ya zama abin zargi.
"Jami’ai da sojoji na rundunar Sojin Najeriya da aka tura zuwa yankuna daban-daban na ayyukan tsaron cikin gida suna kan tsaftataccen aikinsu kuma suna kan hanyoyi masu cutarwa don kiyayewa da kare kasar daga masu niyyar lalata ta.
Bayan kokawa kan yadda 'yan Najeriya ke watsa hotunan a kafafen sada zumunta, Yerima ya bayyana matakin da rundunar zata dauka.#
"Sojojin Najeriya sun dauki wannan mummunan dabi'a ta rashin kishin kasa sam-sam ba abar yarda ba kuma daga yanzu za ta dauki matakan doka don kare sojojin da suka mutu a fagen yaki daga yi musu ba'a a kafafen sada zumunta ko kuma wani dandali."
KU KARANTA: Majalisar Dattawa Ta Nemi Ganawa da Shugaba Buhari Cikin Gaggawa kan Matsalar Tsaro
A wani labarin daban, Gwamnan jihar Yobe kuma shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC, a ranar Lahadi ya gana da shugaban hafsoshin tsaro Janar Leo Irabo don tattauna batun harin Boko Haram a Geidam.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Darakta Janar na harkokin yada labarai ga Gwamnan, Mamman Mohammed ya sanya wa hannu a ranar Lahadi, Vanguard News ta ruwaito.
Mohammed ya ce, tun daga ranar Juma'a ne Buni ya kasance yana tattaunawa da jami'an tsaro don samar da mafita mai dorewa game da kai hare-hare a kan Geidam da al'ummomin kan iyaka.
Asali: Legit.ng