Dalilin da yasa aka haramta yin tashe a Kano

Dalilin da yasa aka haramta yin tashe a Kano

A daidai lokacin da ake tsaka da azumin watan Ramadana, an dade da fara tashe a wasu jihohin arewa, wanda ya kasance daya daga cikin al’adun kasar Hausa a cikin wata mai tsarki.

Bisa al’da da zaran an kai azumi 10 na farko, kananan yara da ma wasu manya kan fita yin wasannin barkwanci da sunan tashe, inda za a dunga basu kyaututtuka.

Sai dai a jihar Kano wadda take a matsayin daya daga cikin manyan yankuna na kasar Hausa, abin ya sha bambam.

Domin kuwa kamar yadda ta faru a wasu shekarun baya, a wannan karo ma hukumomi a jihar sun haramta gudanar da wannan al'ada mai dinbin tarihi.

Dalilin da yasa aka haramta yin tashe a Kano

Dalilin da yasa aka haramta yin tashe a Kano
Source: UGC

A halin da ake ciki, tuni rundunar 'yan sandan jihar ta Kano ta ce za ta dauki tsattsauran mataki kan duk wani da aka kama ya taka dokar hana yin tashe a jihar.

Kakakin yan sandan jihar, DSP Haruna Kyawa ya ce jami'an 'yan sanda na yin sintiri a cikin dare domin tabbatar da cewa ba a bari masu neman tayar da fitina sun cimma burinsu ba.

Ya ce: "ba wai tashen ne laifi ba, a'a. Amma bata gari da suke bin 'yan tashen suke fakewa da haka suke yin kwace da sauran miyagun laifi shi ne ba ma so."

KU KARANTA KUMA: Matashi ya fille kan abokinsa ya kai ma boka don ayi masa kudin tsafi

Ya kuma jadadda cewa jami'ansu za su dunga sintiri a kewayen jihar tun daga lokacin sallar magariba zuwa karfe goma na dare don kama wadanda karya doka.

A wani lamari na daban, mun ji cewa akalla mutum guda ne ya rigamu gidan gaskiya, yayin da wasu da dama suka samu munana raunuka sakamakon wani mummunan hari da wasu yan bindiga suka kai a wani gidan kallon kwallo dake garin Jos na jahar Filato.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya auku ne a ranar Asabar, yayin da ake buga kwallon wasan karshe na kofin FA na kasar Ingila tsakanin kungiyar Manchester City da Watford, inda Manchester ta lallasa Watford 6-0.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel