Da Dumi-Dumi: ’Yan Bindiga Sun Bankawa Babbar Kotun Tarayya Dake Ebonyi Wuta

Da Dumi-Dumi: ’Yan Bindiga Sun Bankawa Babbar Kotun Tarayya Dake Ebonyi Wuta

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun cinna wa Babban Kotun Tarayya na Abakaliki, Jihar Ebonyi, yankin Kudu maso Gabashin Najeriya wuta.

Ginin yana kan babbar hanyar Enugu/Abakaliki, daura da ofishin jam'iyyar PDP ta jihar.

Wasu ‘yan bindiga ne sukai amfani da bama-bamai suka kai harin a ranar Talata, kamar yadda wata majiya ta shaida wa wakilin Premium Times.

Da Dumi-Dumi: ’Yan Bindiga Sun Bankawa Babbar Kotun Tarayya Dake Ebonyi Wuta
Da Dumi-Dumi: ’Yan Bindiga Sun Bankawa Babbar Kotun Tarayya Dake Ebonyi Wuta Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Gobarar wadda ta fara da sanyin safiyar yau ta shafi dakin karatu da kuma ofishin tsaro na kotun.

Sai dai an ce daga baya jami’an kashe gobara sun tattara zuwa wurin don kashe gobarar kafin ta sake yin barna.

Babu wani wanda ya mutu a harin wanda ya lalata bayanan kotu da dama a dakin karatun.

Kakakin yan sanda a jihar, Loveth Odah, ta tabbatar da faruwar lamarin. Ta ce maharan sun zo da yawansu don kai harin.

Karin bayani nan gaba...

Asali: Legit.ng

Online view pixel