Yanayin Tsaro Babu Dadi, Ya Kamata a Fadawa Buhari Gaskiya – Zulum

Yanayin Tsaro Babu Dadi, Ya Kamata a Fadawa Buhari Gaskiya – Zulum

- Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya koka kan halin da yanayin tsaro yake ciki a yankin arewa maso gabas

- Zulum ya ce sam lamarin babu dadin ji kuma hakki ne da ya rataya a wuyansa fadawa shugaban kasa Buhari gaskiyar halin da ake ciki

- Gwamnan ya bayyana cewa akwai bukatar su nemi taimakon kasashen waje wajen kawo karshen ta'addanci a Najeriya

Babagana Zulum, gwamnan Borno, ya ce hakkinsa ne ya bari shugaban kasa Muhammadu Buhari ya san gaskiya game da yanayin tsaro a arewa maso gabas.

Sama da shekaru goma, yankin na ci gaba da fuskantar hare-hare daga maharan Boko Haram.

A baya-bayan nan maharan sun kaddamar da wasu hare-hare, musamman a duk fadin garuruwan Borno, inda suka kashe mazauna garin da dama.

Yanayin Tsaro Babu Dadi, Ya Kamata a Fadawa Buhari Gaskiya – Zulum
Yanayin Tsaro Babu Dadi, Ya Kamata a Fadawa Buhari Gaskiya – Zulum Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Har ila yau, suna ta kai hare-hare kan sansanonin soji a yankin.

Jaridar The Cable ta ruwaito yadda aka kashe wani jami'i da sojoji shida a Mainok lokacin da maharan suka kai hari ranar Lahadi.

KU KARANTA KUMA: APC Za Ta Yi Mulki Har Bayan 2023, 'Yan Najeriya Suna Son Jam'iyyar Mai Mulki, Inji Tinubu

Da yake zantawa da manema labarai bayan ganawa da shugaban a daren Litinin, Zulum ya ce akwai bukatar neman taimako don magance ta’addanci a yankin.

Gwamnan ya nuna nadamar sa kan yadda daruruwan mutane suka kaurace wa gidajen su, lamarin da ya mai da garuruwa da dama kufai.

“A Borno, musamman, an kai hari hedikwatar Sojoji da yawa, an kashe hafsoshin sojojin Najeriya,” in ji shi.

“Bari na yi amfani da wannan dama domin mika ta’aziyyata ga iyalan mamatan. Allah ya gafarta musu.

“Ina ganin hakki ne da ya rataya a wuyana in zo in fada wa Shugaban Kasa gaskiya; ya san abin da ke gudana a cikin dukkan yankin na arewa maso gabas.

“Ina ganin akwai bukatar mu samu taimako domin mu yi nasara a wannan yaki da masu tayar da kayar baya. Lamari ne mai matukar ban tausayi.

“Kwanakin baya, an kai wa Damasak hari; daruruwan mutane sun fara arcewa daga Damasak, kuma yanzu Geidam ya kusan zama ba kowa. Mutane da yawa sun bar Geidam."

Gwamnan ya kuma dora alhakin matsalar tsaro a yankin arewa maso gabas kan rashin kayan aikin soji yana mai cewa, "Ina ganin har yanzu sojoji ba su karbi wasu kayan aikin da suka yi oda ba."

KU KARANTA KUMA: Rashin Tsaro: Gwamnonin Najeriya 2 Sun Saka Dokar Kulle a Jihohinsu

A gefe guda, mun ji cewa sanatoci da gwamnoni uku a ranar Talata sun nuna damuwa game da kashe-kashe da sace-sacen mutane a kasar, suna masu rokon Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya nemi taimakon kasashen waje.

'Yan majalisar, yayin da suke tattaunawa kan wani kudiri kan ayyukan kungiyar Boko Haram a jihar Neja, sun bayyana rashin tsaro a kasar a matsayin abin kunya.

Sanata Sani Musa (All Progressives Congress, Neja ta gabas) ne ya dauki nauyin kudirin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel