Rashin tsaro: Ka yafewa 'yan Najeriya da suka dinga zaginka, J. Martins ga Jonathan

Rashin tsaro: Ka yafewa 'yan Najeriya da suka dinga zaginka, J. Martins ga Jonathan

- Fitaccen mawakin nan Martin Okwun, wanda aka fi sani da J. Martins, ya roki yafiya daga wurin Goodluck Jonathan

- Ya ce tsohon shugaban kasan Najeriya ya jure caccaka da kalubale tare da zagin da jama'a suka dinga masa

- Ya ce hatta rashawa da gwamnatin Buhari ke ikirarin yaki da ita, karuwa kawai take yi fiye da zamanin Jonathan

Martin Okwun, mawakin da aka fi sani da J. Martins, ya roki Goodluck Jonathan, tsohon shugaban kasan Najeriya da ya yafewa 'yan Najeriya da suka ci amanarsa tare da kiransa da miyagun sunaye yayin mulkinsa.

Mawakin yana kwatanta yanayin rashin tsaro karkashin mulkin tsohon shugaban kasan da kuma na wanda ya gaje shi, Muhammadu Buhari, a wata wallafarsa ta Instagram a ranar Talata.

Jonathan ya sha mugun kaye a kokarinsa na zarcewa mulkin kasar nan wa'adi na biyu, a hannun dan takarar jam'iyyar APC.

Masu caccakarsa a wancan lokacin sun ce bai yi kokari ba wurin shawo kan matsalar tsaron da kasar nan ke fuskanta.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Rikici ya barke a Legas, ana harbe-harbe kusa da LASU

Rashin tsaro: Ka yafewa 'yan Najeriya da suka dinga zaginka, J. Martins ga Jonathan
Rashin tsaro: Ka yafewa 'yan Najeriya da suka dinga zaginka, J. Martins ga Jonathan. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Mainok: Zulum yayi ta'aziyyar sojojin da suka rasu, ya jajantawa iyalan da hari ya shafa

Amma Buhari yana fuskantar makamancin lamarin a halin yanzu inda 'yan Najeriya ke kokawa a kan yaduwar rashin tsaro da sauran kalubale da kasar nan ke fuskanta.

Kamar yadda mawakin ya sanar, 'yan Najeriya suna samun tsaro tare da 'yancin fadin abinda ke ransu a karkashin mulkin Jonathan fiye da mulkin yanzu.

Hakazalika, mawakin ya zargi cewa a fannin rashawa, an zargi gwamnatin Jonathan da cin rashawa amma a halin yanzu kara yawa take yi.

A wani labari na daban, kamar yadda rahotanni suka bayyana, 'yan Boko Haram sun kai farmaki karamar hukumar Gwoza dake jihar Borno a ranar Litinin da dare.

Kamar yadda jama'a da dama suka wallafa a shafinsu na Twitter, mayakan sun isa garin wurin karfe takwas na dare kuma suka dinga sakin ruwan wuta.

Kungiyar masu tsaurin ra'ayin ta shiga garin Gwoza a ranar 26 ga watan Afirilun 2021 inda suka dinga harbe-harbe yayin da mazauna yankin suka dinga tserewa zuwa tsaunika domin neman wurin buya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng