Tashin hankali: 'Yan daba sun fi karfin 'yan sanda, sun kone ofishinsu a Sokoto

Tashin hankali: 'Yan daba sun fi karfin 'yan sanda, sun kone ofishinsu a Sokoto

- Jihar Sokoto na daga cikin jihohin arewa da suka fara fuskantar babban kalubale na tsaro

- Wasu gayyar 'yan daba a jihar arewa maso yamman sun kai hari ofishin 'yan sandan inda suka kone shi

- 'Yan daban sun kone har da motar wani babban dan sanda tare da motocin sintiri guda biyu da aka ajiye a ofishin

A ranar Talata, 27 ga watan Afirilun 2020, 'yan daba a jihar Sokoto sun kone ofishin 'yan sanda dake karamar hukumar Kware ta jihar.

Gungun 'yan daban da suka kunshi matasa, sun isa ofishin 'yan sandan inda suka dinga ihu tare da jaddda cewa akwai wasu wadanda aka kama da laifin garkuwa da mutane amma aka sake su.

'Yan daban sun fi karfin 'yan sandan inda suka rinjayi jami'an tsaron dake gadin ofishin kuma suka koneshi tare da motar DPO da kuma motocin sintiri guda biyu.

KU KARANTA: Mainok: Zulum yayi ta'aziyyar sojojin da suka rasu, ya jajantawa iyalan da hari ya shafa

Tashin hankali: 'Yan daba sun fi karfin 'yan sanda, sun kone ofishinsu a Sokoto
Tashin hankali: 'Yan daba sun fi karfin 'yan sanda, sun kone ofishinsu a Sokoto
Asali: Getty Images

KU KARANTA: Borno: Soji sun ragargaza yaran kwamanda Abou Muhammad da suka kai farmaki Gwoza

Ya kara da cewa matasan sun yi nasarar kashe daya daga cikin wandanda ake zargin kuma sun raunata wani.

Rundunar 'yan sandan jihar Sokoto ta tabbatar da aukuwar lamarin ta bakin kakakinta, ASP Abubakar Sanusi.

Sanusi ya sanar da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya cewa an kama wadanda ake zargin tun farko ne bayan binciken da aka yi aka gano da hannunsu a wata garkuwa da mutane da aka yi a yankin.

Lamarin ya auku ne bayan kwanaki kadan da hukumar 'yan sandan jihar Kebbi ta tabbatar da kisan jami'anta tara a karamar hukumar Sakaba ta jihar.

A wani labari na daban, Opeyemi Bamidele, sanata mai wakiltar mazabar Ekiti ta tsakiya, yace bashi da tabbacin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya san halin da tsaron kasar nan ke fuskanta.

Bamidele ya sanar da hakan a ranar Talata a tsakar majalisar dattawa yayin bada gudumawa a kan wata bukata da Mohammed Sani Musa, sanata mai wakiltar Neja ta gabas ya bijiro da ita.

Musa ya janyo hankalin majalisar a kan rahoton na kafa tutocin da Boko Haram suka yi a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja, The Cable ta wallafa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel