Mainok: Zulum yayi ta'aziyyar sojojin da suka rasu, ya jajantawa iyalan da hari ya shafa

Mainok: Zulum yayi ta'aziyyar sojojin da suka rasu, ya jajantawa iyalan da hari ya shafa

- Gwamna Babagana Umara Zulum ya yi ta'aziyya tare da jaje ga iyalan sojoji da jama'ar da suka rasa rayukansu a Mainok

- Ya jinjinawa sadaukai kuma zakakuran sojin a kan sadaukar da rayukansu da suka yi wurin baiwa jihar kariya

- A cikin ranakun karshen mako ne 'yan ta'adda suka dira garin Mainok mai kusanci da babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya mika ta'aziyyarsa da jajensa ga iyalan sojojin da suka rasu a cikin kwanakin karshen mako yayin yaki da 'yan ta'addan Boko Haram a garin Mainok dake kan babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

Zulum a wata takarda da ya fitar ta hannun kakakinsa, Malam Isa Gusau, ya kwatanta sojojin da suka rasa rayukansu a matsayin sadaukai wadanda suka mutu yayin kare Borno da kuma karfin ikon kasar nan.

"Ba tare da duba da abinda ya faru a Mainok ba da kuma yadda ya faru, dole ne mu yi kokarin duba sadaukantaka ta sojojin da suka rasa rayukansu yayin baiwa kasar nan kariya. Iyaye ne kuma a halin yanzu 'ya'yansu marayu ne. Matansu yanzu sun rasa mazajensu kuma iyalansu sun rasa 'yan uwa.

KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun kutsa jihar Ribas, sun sheke jami'an tsaro 4

Mainok: Zulum yayi ta'aziyyar sojojin da suka rasu, ya jajantawa iyalan da hari ya shafa
Mainok: Zulum yayi ta'aziyyar sojojin da suka rasu, ya jajantawa iyalan da hari ya shafa. Hoto daga @GovZulum
Asali: Twitter

KU KARANTA: An kama miyagun ƙwayoyi cikin mutum-mutumin Maryama mahaifiyar Yesu

"Sojoji ne daga rundunar sojinmu da suka zaba sadaukar da rayukansu wurin bamu kariya da kuma kare martabar kasarmu. Muna makokin sojojinmu da kuma duk wanda al'amarin Mainok ya ritsa dashi.

"Muna jinjina ga wadannan sadaukan da suka rasa rayukansu kuma muna musu fatan samun rahama. Muna mika ta'aziyya ga iyalansu da kuma rundunar sojin kasar nan," cewar Zulum.

A wani labari na daban, dakarun sojin hadin guiwa karkashin Operation Whirl Stroke a ranar Asabar sun damke dagacin Cha (Mue Ter Cha) Utambe Adzer dake karamar hukumar Ukum ta jihar Binuwai bayan samun miyagun makamai da harsasai a fadarsa.

An gano cewa dakarun sun samu wasu makamai a fadar dagacin Lumbuv, Teran Kwaghbo a yankin kuma sun yi yunkurin kama shi amma ya tsere.

Wata majiya daga yankin da ta bukaci a boye sunanta ta sanar da Vanguard cewa dakarun OPWS sun yi aiki ne da wasu bayanan sirri inda suka gano makaman a fadar sarakunan biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: