NAF ta bayyana Matakin da zata ɗauka kan zargin da ake mata na kai hari ta sama kan sojoji a Mainok

NAF ta bayyana Matakin da zata ɗauka kan zargin da ake mata na kai hari ta sama kan sojoji a Mainok

- Rundunar sojin sama NAF ta maida martani kan wani rahoto da ake yaɗawa a kafar sada zumunta cewa sun kai hari ta sama kan sojoji a garin Mainok dake Jihar Borno

- Rahoton ya bayyana cewa jami'an NAF ɗin sun kai harin ne bisa kuskure, kuma sama da sojojin Najeriya 20 ne suka rasa rayukansu a cewar rahoton

- NAF ta bayyana cewa ta ƙaddamar da bincike kan lamarin kuma za'a sanar da jama'a duk sakamakon da binciken ya nuna da zaran an kammala

Rundunar sojin sama (NAF) tayi martani ga wani zargi da ake mata cewa ta kai hari kan sojoji a garin Mainok, jihar Borno kamar yadda Punch ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Tsohon Sufetan Yan Sanda Ya Bayyana Hanyar da Gwamnati Zata Bi Ta Magance Matsalar Tsaro

Rahoton ya bayyana cewa sama da jami'an soji 20 ne suka rasa rayukansu a harin da wani jirgin yaƙin sojin sama yakai Mainok, Maiduguri bayan masu kula da jirgin sun yi kuskure wajen kai hari ga mayaƙan Boko Haram.

A wani saƙo da NAF ta fitar a dandalin sada zumunta na tuwita, tace Za'a gudanar da bincike a kan lamarin kuma za'a sanar da mutane sakamakon da aka samu da zaran an kammala.

Sojojin Sama sun bayyana Matakin da zasu ɗauka kan zargin da ake musu na kai hari kan sojoji a Mainok
Sojojin Sama sun bayyana Matakin da zasu ɗauka kan zargin da ake musu na kai hari kan sojoji a Mainok Hoto: punch.ng
Asali: UGC

Saƙon da NAF ɗin ta fitar yace:

"Mun fahimci rahoton dake yawo cewa NAF ta yi sanadiyyar mutuwar sojoji sama da 20 a wani hari da aka kai ta sama a Mainok, wanda yake da nisan kilomita 55 daga Maiduguri."

KARANTA ANAN: Sanata Ali Ndume ya faɗawa gwamnatin tarayya matakin da yakamata ta ɗauka kan masu ɗaukar Nauyin Boko Haram

"NAF na sanar da cewa za'a gudanar da bincike kan rahoton da ake ta yaɗawa, kuma za'a sanar da jama'a sakamakon binciken da zarar an kammala."

"Duk wani mai wata tambaya ko neman ƙarin bayani, to ya tuntuɓi ofishin mai magana da yawun rundunar NAF dake Hedkwatar su."

A Wani labarin kuma Yan Najeriya na samun wutar Lantarki, Gwamnatin tarayya tayi watsi da rahoton bankin duniya

Gwamnatin tarayya tayi watsi da rahoton bankin duniya wanda ya nuna cewa mafi yawancin yan Najeriya na samun wutar lantarki ƙasa da awanni 12 a rana.

Mai baiwa shugaban ƙasa shawara ta musamman kan kayayyakin gwamnati, Mr. Ahmad Rufai Zakari, shine ya bayyana haka yayin da yake martani kan rahoton.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262