Haramun Ne Yin Kasuwancin Bitcoin, in Ji Shehin Malami Daga Kano

Haramun Ne Yin Kasuwancin Bitcoin, in Ji Shehin Malami Daga Kano

- Fitaccen malamin addinin Islama ya bayyana haramcin ta'ammuli da kudaden crypto

- A cewarsa, kudi ne da ba hankali a ciki, domin kuwa ba kasar da ta yarda dasu a duniya

- Hakazalika ya ce shi kansa wanda ya kirkiro shi yakan nisanta kansa da kudaden na crypto

Fitaccen malamin Musulunci daga jihar Kano, Sheikh Muhammad Bin Uthman ya ce kasuwancin kudaden intanet na cryptocurrency haramun ne a Musulunci, Aminiya ta ruwaito.

Sheikh Bin Uthman ya kuma shawarci jama’a da su guji harkar saboda illar da ke tattare da ita, kasancewar yawanci ana shiga harkar ne da ganganci ko kuma a jahilce.

Shehin malamin wanda kuma shi ne Babban Limanin Masallacin Juma’a na Sahaba da ke unguwar Kundila a Kano, ya ba da fatawar ne yayin wani karatu da ya gabatar mai taken ‘Hakkokin Musulmi Guda Shida’ a ranar Lahadi.

KU KARANTA: 'Yan Bindiga Sun Hallaka Wani DPO da Jami’ansa 8 a Wata Jihar Arewacin Najeriya

Haramun ne yin kasuwancin Bitcoin, in ji Shehin Malami daga Kano
Haramun ne yin kasuwancin Bitcoin, in ji Shehin Malami daga Kano Hoto: trustetc.com
Asali: UGC

A cewar malamin, “Shi kansa wanda ya kirkiro kudin [Satoshi Narcomoto] yana musanta cewa shi ne ya kirkiro tsarin, to ka ga ta fuskar asali ma ana kai-kawo kan wanda ya kirkiro shi.”

A kan haka ne ya ja hankalin Musulmai da su kaurace wa shiga tsarin, duba da irin hatsarin da ke tattare da shi.

“A farkon fitowarsa, duk Bitcoin yana daidai da Senti daya na Amurka, yanzu kuma kowanne daya sai ka ba da Dalar Amurka 11,000 za a ba ka. Ka ga abin ai ya zama hauka.

“Kuma wannan kudi idan ka ce za ka yi harka da su, idan suka karye ba wanda za ka kama ka ce ya biya ka, tunda babu wata kasa da ta yarda da shi don haka ba kudi ba ne,” inji shi.

KU KARANTA: 'Yan Bindiga Sun Hallaka Wani DPO da Jami’ansa 8 a Wata Jihar Arewacin Najeriya

A wani labarin, Ofishin shiyyar Ibadan na Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Zagon Kasa (EFCC) ya kama wani dan kasuwar bitcoin da laifin aikata zamba a yanar gizo, Premium Times ta ruwaito.

Wanda ake zargin, Ayomide Adebowale, an kama shi a ranar Juma’a, tare da wasu mutum hudu daga wasu wurare biyu a yankin Elebu da ke Ibadan ta Jihar Oyo.

Kakakin EFCC, Wilson Uwujaren, ya bayyana sauran da aka kama da suna Philip Gabriel, Mayowa Jolaoso Segun, Babatunde Segun Adeyinka da Abiodun Tolulope Emmanuel.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel