Da Dumi-Dumi: ’Yan Bindiga Sun Afka Gidan Sojoji Sun Kashe 5 a Rivers
- 'Yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai harin gidan da sojoji ke zama a Rivers sun bude musu wuta
- Rahotanni sun ce 'yan bindigan sun taho ne daga tsallaken wani rafi a karamar hukumar Abia na jihar Rivers suka nufi gidan sojojin kai tsaye
- Kawo yanzu, mai magana da yawun sojoji na Division 6 a Port Harcourt, Manjo Charles Ekeocha bai tabbatar da afkuwar lamarin ba domin bai daya wayarsa ba
Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe kimanin sojoji biyar a Omelema da ke karamar hukumar Abia a jihar Rivers, The Punch ta ruwaito.
An gano cewa yan bindigan sun taho ne daga wani rafi da ke kusa, suna harbe-harbe sannan suka wuce gidan da sojojin suke suka bude musu wuta, biyu suka mutu nan take misalin karfe 11 na daren ranar Litinin.
DUBA WANNAN: Da duminsa: Ƴan bindiga sun afka jami'a sun sace ɗalibai a Makurɗi
Wannan harin ne zuwa ne kwanaki biyu bayan wasu yan bindigan da ake zargin yan IPOB ne suka kai wa wasu jami'an tsaro hari suka kashe takwas cikinsu.
Kakakin Division 6, Rundunar Sojojin Nigeria da ke Port Harcourt, Manjo Charles Ekeocha bai tabbatar da afkuwar lamarin ba kawo yanzu domin baya amsa wayarsa a lokacin hada wannan rahoton.
KU KARANTA: Da Ɗuminsa: Ƴan IPOB Sun Yi Wa Makiyaya Fulani 19 Yankan Rago a Anambra
A hannu guda, Dukkan shugabannin hukumomin tsaro a ranar Litinin sun yi taron gaggawa na tsaro a hedkwatar rundunar yan sanda da ke Moscow Road a Port Harcourt.
A wani rahoton daban, Mallam Garba Shehu ya caccaki wadanda suke sukar Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Dr Isa Pantami saboda rashin yafe masa abin da ya yi a baya, Channels Television ta ruwaito.
Ya na ganin rashin yafewa ministan kan maganganun da ya yi na goyon bayan kungiyoyi masu tsatsauran ra'ayi ya fi muni kan laifin da ministan ya aikata.
Babban mai taimakawa shugaban kasar a bangaren watsa labarai ya yi wannan kalaman ne a lokacin da ya bayyana a shirin Politics Today na Channels Television a ranar Juma'a.
Asali: Legit.ng