Jerin Kasashen da Suka Mance da Labarin Maleriya Tsawon Shekaru 20
- A ranar Lahadi ne aka yi bikin yaki da ranar zazzabin cizon sauro ta duniya, cuta mai kisa
- Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana cewa, cutar tana kisan mutane sama 400,000 a shekara
- Hukumar lafiya ta duniya ta jero wasu kasashe da suka mance da labarin zazzabin cizon sauro
A yau ranar Lahadi ake bikin yaki da cutar zazzabin cizon sauro da aka fi sani da Maleriya, cutar da ke da alhakin hallaka dubban mutane musamman kananan yara a duniya.
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta bayyana cewa, a duk minti daya zazzabin cizon sauro na kashe yaro daya a duniya.
WHO ta bayyana haka ne a yayin da ake bikin ranar yaki da cutar zazzabin ciwon sauro ta duniya.
Hukumar ta ce a shekarar 2019 cutar zazzabin cizon sauro da aka fi sani da maleriya ta kashe kusan mutum 400,000 a kasashe 87, kuma ta fi kashe yara 'yan kasa da shekara biyar.
KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun hari coci, sun kashe likita, sun sace mutane Kaduna
Albarkacin ranar, WHO ta bayyana jerin kasashe 11 da ba su san labarin cutar maleriya ba tsawon shekaru 20.
Kasashen sun hada da Algeria, Argentina, Armenia, El Salvador, Kyrgystan, Morocco, Paraguay, Sri Lanka, Turkmenistan, Daular Larabawa da kuma Uzbekistan.
KU KARANTA: Gwamnatin Zamfara ta haramta sayar da man fetur a wasu yankuna saboda 'yan bindiga
Ya bayyana cewa daga cikin jimillar kudin, kasar na bukatar sama da naira biliyan 350 don yaki da cutar a shekarar 2021 kadai.
Ehanire, Ministan Lafiya, ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a wani taron manema labarai a babban birnin tarayya Abuja.
Asali: Legit.ng