Gwamnatin Zamfara ta haramta sayar da man fetur a wasu yankuna saboda 'yan bindiga
- Gwamnatin jihar Zamfara ta gaggauta haramta sayar da man fetur da sauran nau'ukansa a sassan jihar
- Gwamnati ta umarni kungiyoyi dake da alaka da sayar da albarkatun man fetur da su bi dokar ta yanzu
- Hakazalika an umarci jami'an tsaro su tabbatar da bin doka da oda na haramcin da gwamnatin ta fitar
Gwamnatin Zamfara ta haramta sayar da albarkatun man fetur a yankunan da hare-hare suka yi kamari a 'yan kwanakin nan a jihar, Vanguard ta ruwaito.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai na jihar, Alhaji Ibrahim Dosara, wanda aka fitar a Gusau ranar Asabar.
Dosara ya bayyana cewa matakin "ci gaba ne kan kokari da kuma matakan da gwamnatin jihar Zamfara ke dauka na magance matsalar 'yan ta'adda da ta dabaibaye jihar."
Ya bayyana sunayen yankunan da abin ya shafa kamar haka: Wanke, Magami, Dansadau, Dangulbi, Dankurmi, Bindin, Munhaye, Kizarah, Kunchin Kalgo da kewaye.
KU KARANTA: EFCC Ta Kwamushe Wani Dan Kasuwa Mai Hada-Hadar Bitcoin Bayan Haramtata
A cewar kwamishinan, haramcin zai fara aiki ne nan take kuma zai ci gaba har zuwa wani lokaci.
Ya bayyana cewa dole ne duk masu hada-hadar bakar kasuwa ta man fetur su dakatar da sayar da kayayyakin man fetur a yankunan da abin ya shafa.
“Ana gargadin dukkanin gidajen mai da ke cikin wuraren da abin ya shafa da su daina sayar da kayayyakin mai ga wadanda suke zuwa da gwangwani ko kuma wani mazubi.
“Motoci masu motsi ne kawai aka yarda su sayi kayayyakin man fetur daga gidajen mai, daga yanzu.
Dosara ya ce "An ba NUPENG da sauran kungiyoyi kan albarkatun man fetur su umarci mambobinsu da su guji duk wani abin da zai kawo cikas ga wannan umarnin na gwamnati.
Kwamishinan ya ce, gwamnati ta umarci hukumomin tsaro da su tabbatar an bi doka da oda tare da cafke duk wanda aka samu da karya wannan umarni.
KU KARANTA: Fadar shugaban kasa ta fayyace banbanci tsakanin batun Minista Pantami da Adeosun
A wani labarin daban, Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya gargadi 'yan bindiga a jihar da su tuba ko kuma su fuskanci mummunan mataki daga gwamnati.
Gwamnan a ranar Asabar, 24 ga Afrilu, ya bayyana cewa ya tsara sabuwar taswira a yadda yake tunkarar matsalar tsaro da ke addabar jihar, a cewar wata sanarwa daga mai magana da yawunsa, Yusuf Gusau, Channels TV ta ruwaito.
Matawalle ya bayyana cewa dakatarwar da aka yiwa wani hakimi a masarautar Shinkafi kwanan nan saboda hada kai da 'yan bindiga yana daya daga cikin sabbin matakan da ya yanke shawarar aiwatarwa.
Asali: Legit.ng